Banci nanin ba nanin baza ta cini ba: Babu wanda na yiwa alkawarin motoci 10 idan Buhari yayi nasara - Dino Melaye

Banci nanin ba nanin baza ta cini ba: Babu wanda na yiwa alkawarin motoci 10 idan Buhari yayi nasara - Dino Melaye

- Babu wanda na yiwa alkawarin mota idan Atiku ya samu nasara a kotun shari'ar zaben shugaban kasa

- Wannan magana dai ta fito daga bakin Sanata Dino Melaye ne, wanda yake wakiltar jihar Kogi ta Yamma

- Wani shafi na bogi da yake yawo a Twitter ya wallafa wani rubutu da yake nuni da cewa Sanatan yayi alkawarin bayar da motoci guda goma idan Atiku ya samu nasara a kotu

Sanata Dino Melaye ya nesanta kanshi daga wani alkawari da yake nuni da yace zai bayar da motoci guda goma idan har Atiku ya samu nasara akan Buhari a kotu.

Wani shafin Twitter da yake nuni da kamar na Sanatan ne yayi alkawarin bayar da motoci idan Alhaji Atiku Abubakar ya samu nasara a kotun shari'ar zaben shugaban kasa.

Shafin wanda aka gano na karya ne ya wallafa rubutu kamar haka:

"Yau za'a bayyana sakamakon zabe a kotu, lokaci bai kure ba idan nace zan bayar da motoci kirar Honda Pilot guda goma, kuyi magana ku kuma bayyana irin kalar da kuke so. Zan zaba wanda zan bawa."

KU KARANTA: Abubuwa sai Lahaula a Saudiyya: An kama babban Malami a Saudiyya da ya nuna rashin jin dadin shi dangane da badalar da ake yi a kasar

Sai dai kuma Sanatan na jihar Kogi ya shiga ainahin shafinsa na gaskiyar ya karyata wannan labari na kanzon kurege na cewa zai bayar da wadannan motoci idan Atiku Abubakar ya samu nasara akan shugaban kasa Muhammadu Buhari a shari'ar zaben shugaban kasa da aka yi a ranar 23 ga watan Fabrairun wannan shekarar.

Sanatan ya wallafa rubutun kamar haka:

"Shafin karya ne 'yan 419 ne, babu wanda na yiwa alkawarin zan bawa komai akan wannan lamarin."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel