Dangote ya bayyana shirin taimakawa masu yi masa ciniki a Najeriya

Dangote ya bayyana shirin taimakawa masu yi masa ciniki a Najeriya

A cikin farkon makon nan mu ka ji cewa Shugaban kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya bayyana shirin kamfanin simintinsa na taimakawa jama’a ta hanyar inganta tattalin arzikinsu.

Rahotanni sun ce Kamfanin Dangote ya nuna a shirya yake wajen habaka tattalin arzikin miliyoyin jama’a. Kamfanin ya bada wannan babban albishir ne wajen wani biki da ya shirya.

Dangote ya yi wannan alkawari ne ta bakin babban Darektansa, Olakunle Alake, wanda ya wakilce sa a bikin da aka shirya domin bada kyauta ga wanda su ka yi nasara a gasar da aka yi.

Alake yake cewa kamfanin na Dangote zai bada kyaututtuka iri-iri ga mutane miliyan 21 a Najeriya. Wadannan kyaututtuka da za a raba za su taimaka wajen inganta halin rayuwar mutane.

Hukumar dillacin labarai na kasa ta ce kamfanin sun shirya wannan kyauta ne domin sakawa masu yi mata ciniki ta hanyar amfani da simintin Dangote wajen yin gine-gine a Najeriya.

KU KARANTA: Kotun zaben shugaban kasa ta yi watsi da babban korafin Buhari

Darektan kamfanin kasar ya ce sun bi a hankali wajen tantance wadanda za a rabawa wadannan kyaututtuka. Alade ya ce duk sun yi wannan ne saboda sha’awar su na ganin sun taimaki mutane.

A na ta bangaren, Darektan kasuwanci na kamfanin simintin, Funmi Sanni, ta ce an shirya wannan garabasa ne saboda a godewa wadanda su ka dade su na mu’amala da wannan kamfani.

Kawo yanzu wasu sun tashi da manyan kyaututtukan da ba su yi tsammani ba. Daga cikin manyan kyautan da aka raba akwai motoci. Ana sa rai cewa mutane 43 ne za su tashi da mota.

A wannan biki da aka shirya, wasu sun samu babara na zamani da kuma motar nan mai taya uku wanda aka fi sani da keke napep. Haka zalika an rabawa wasu talabijin da na’urorin ruwan sanyi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel