Abunda Buhari ya fada ma ministocinsa a zaman majalisa na yau

Abunda Buhari ya fada ma ministocinsa a zaman majalisa na yau

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa a yau, Laraba, 11 ga watan Satumba, karo na farko tun bayan dawowarsa mulki a wa'adi na biyu.

An soma zaman ne da misalin karfe 11:00 na safe a zauren majalisar zartarwa da ke fadar shugaba kasa Abuja, an gabatar da taken kasa amman ba tare da addu’ar bude taro ba da aka saba yi.

A wani takaitaccen jawabi, Shugaban kasa Buhari ya bukaci ministocinsa da ka da su nuna gazawa ga yan Najeriya musamman akan al’amuran da suka yi sanadiyar zaban gwamnatinsa, kamar inganta tsaro, bunkasa tattalin arziki da nuna gaskiya, da kuma kau da rashawa.

Yace yana bukatan su karfafa kwazonsu a wannan karo na biyu su kuma yi aiki cikin lumana, inda ya karfafa cewa tattaunawa da hadin kai wajen gudanar da ayyuka ne matattakalan nasara.

Yayin da yake musu tuni ga rantsuwar da suka dauka makonni uku da suka gabata, yace dole su yiwa kasarsu hidima.

Daga cikin wadanda suka halarci taron harda mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo; Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha; Shugabar Ma’aikata, Winifred Oyo-Ita da mai ba kasa shawara kan harkokin tsaro, Babagana Monguno.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kotu ta soke jawabin babban shaidan PDP da ke goyon bayan karar Atiku

Idan za ku tuna bayan tabbatar da ministoci 43 da majalisar dattawa ta yi, Shugaban kasar ya rantsar da su a ranar 21 ga watan Agusta, 2019.

Bayan rantsar da ministocin, an basu yan makonni don fahimtar yanda ma’aikatun su ke tafiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel