Ina neman Bilkisu ta bani y’ay’ana 3 tun da ta sake aure – Hassan ya roki kotu

Ina neman Bilkisu ta bani y’ay’ana 3 tun da ta sake aure – Hassan ya roki kotu

Wani magidance dan shekara 45, Hassan Muhammad ya roki wata kotun shari’ar Musulunci dake zamanta a unguwar Magajin Gari cikin garin Kaduna data kwato masa yayansa guda 3 daga hannun tsohuwar matarsa Bilkisu tunda dai ta sake aure.

Rahoton kamfanin dillancin labarum Najeriya, NAN ta bayyana cewa Hassan mazaunin unguwar Rafin Guza na garin Kaduna ya bayyana ma kotun cewa tun da dai Bilkisu ta sake yin wani auren, toh ta ba shi yayansa domin baya son wani mutumi ya yi tarbiyyan yaransa.

KU KARANTA: Kalli ma’aikatun da gwamnan Bauchi ya tura sabbin kwamishinonin jahar guda 20

Sai dai da take mayar da jawabi, Bilkisu Abubakar ta tuna ma kotun cewa ita ta bata daman kulawa da yaran 3 a shekarar 2018 sakamakon tsohon mijinta ya nuna gazawa wajen kulawa dasu.

“A lokacin da na tafi kauye, sai na tarar da yarana cikin mawuyacin hali, biyu daga cikinsu suna fama da matsanancin rashin lafiya, biyu kuma an turasu kungurmin daji don kiwon dabbobi, a haka guda daga cikin yaran ya rasu, kuma ba’a fada min ba har sai da na shigar da mahaifinsu kara.” Inji ta.

Malama Bilkisu ta kara da cewa har yanzu tana zama tare da yayanta, bata tare a gidan sabon mijinta ba, amma duk da haka Hassan ya dage kai da fata sai an bashi yayansa, saboda a cewarsa ya sake yin wani auren, kuma matarsa za ta kula da yaran.

Bayan sauraron dukkanin bangarorin biyu, Alkalin kotun, mai sharia Murtala Nasir ya hana Hassan daukan yayan, inda ya umarci su cigaba da zama da mahaifiyarsu, amma a dinga barinsu su kai masa ziyara a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel