An yanke wa wasu dakarun NAF hukuncin dauri da aiki mai tsanani a gidan yari

An yanke wa wasu dakarun NAF hukuncin dauri da aiki mai tsanani a gidan yari

Rundunar sojin sama ta Najeriya (NAF) ta ce ta tura wasu jami'anta guda biyu gidan yari bayan an gansu a cikin wani faifan bidiyo suna dukan wani farar hula.

A wani faifain bidiyo da ya kewaya a dandalin sada zumunta da wasu kafafen yada labarai na yanar gizo, an ga sojojin biyu suna dukan wani farar hula da bulala.

Ibikunle Daramola, kakakin rundunar NAF na kasa, ya ce an gurfanar da jami'an kuma an tabbatar da sun aikata laifin da ake tuhumarsu da shi.

A wani sako da ya wallafa a shafin rundunar NAF dake Tuwita, Daramola ya bayyana cewa, "an gurfanar da jami'an NAF guda biyu a gaban wata kotun sojoji dake sansanin NAF a Abuja bayan an gansu a cikin wani faifan bidiyo suna dukan wani farar hula a ranar 30 ga watan Agusta. Laifin jami'an ya saba da sashe na 104 na kundin dokokin rundunar soji na shekarar 2004.

"An same su da laifi kuma an yanke musu hukuncin dauri a gidan yarin sojoji tare da horo mai tsanani, wannan hukunci zai taba hatta cigabansu da karin girma a cikin aiki.

DUBA WANNAN: Babbar magana: Kotu ta bayar da umarnin kwace kadarorin tsohon gwamnan APC da matarsa

"An yanke musu hukuncin ne bisa umarnin shugaban rundunar NAF na kasa, Air Marshal Abubakar Sadiq, wanda ya umarci kwamandan sasansanin NAF 053 ya zartar da hukuncin a kan jami'an domin ya zama izina ga masu amfani da aikin soja domin saba doka da bata sunan rundunar NAF," a cewarsa.

Kazalika, Daramola ya bawa 'yan Najeriya tabbacin cewa NAF zata cigaba da tabbatar da cewa dukkan jami'anta na yin aikinsu bisa tsari da biyayya da doka a yayin da suke gudanar da aikin tabbatar da tsaro da cigaban Najeriya.

Daramola ya kara da cewa, Air Marshal Sadiq ya bawa manyan kwamandojin rundunar NAF umarnin gudanar da taro da sojojin dake karkashinsu domin yi musu tuni a kan bukatar yin aiki bisa doka da kuma bukatar kare kima da mutuncin rundunar NAF a duk inda suka tsinci kansu yayin aiki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel