Maigida, mata mai juna biyu, yara 3 da 'yar uwarsu da tazo hutu sun rasa rayukansu bayan cin shinkafa

Maigida, mata mai juna biyu, yara 3 da 'yar uwarsu da tazo hutu sun rasa rayukansu bayan cin shinkafa

- Maigida, mata mai juna biyu, yaransu 3 da 'yar uwarsu da tazo hutu sun rasa rayukansu

- Makwafta na zaton ko dai maganin sauro ne ya kashe su ko kuma shinkafa dafa-duka da suka ci a daren ranar

- Mahaifiyar matar ta rasa ranta sakamakon faduwar da tayi bayan jin labarin mutuwar diyarta da jikokinta

An samu gawarwakin maigida, matarsa mai ciki, yaran sa 3 da 'yar uwarsu da tazo hutu a gida mai lamba 19 Olowora, yankin Mafoloku da ke jihar Legas. An ce iyalan sun ci dafa-dukan shinkafa ne a daren ranar Talata.

Amma kuma, tagwaye masu shekara 4 sun samu kubuta inda suke asibiti a lokacin da muka samu rahoton.

Duk da babu bayanin kwararru a kan mutuwar, ana zaton kodai maganin sauron da su ka sanya ne da dare ko kuma guba a abincinsu.

KU KARANTA: Allah ya yi wa sananniyar mai fassara Al-Qur'ani mai girma rasuwa

Wadanda su ka rasun sun hada da Zakaria wanda aka fi sani da Cool Money; matarsa mai juna-biyu wacce aka fi sani da Iya Aliyah; Aliyah mai shekaru 11; Firdaous mai shekaru 9; Taiwo mai shekaru 4 da Wasilia mai shekaru 17 wacce tazo hutu wurin iyalan.

Majiyar mu ta bayar da rahoton cewa mahaifiyar matar ta fadi ta mutu bayan jin labarin rasuwar diyarta.

Tsohuwar ta kai ziyara ga diyarta inda har mai cikin ta bukaci mahaifiyar da ta kwana a gidan. Tsohuwar taki kwana inda ta tafi Badagry.

Mun gano cewa da wajen karfe 9 na safen jiya Laraba, makwaftansu suka gano cewa babu daya daga cikin iyalan da ya leqo waje daga dakin, wanda hakan bai saba faruwa ba.

Bayan duk yunkurin tashinsu da aka yi ta hanyar kwankwasa kofar, dole ta sa makwaftan suka bude kofar ta karfi. A nan suka samu gawarwaki 7.

Tuni 'yan sanda suka mamaye gidan inda suka tsinci abubuwan da za su bukata don bincike. Gawawwakin kuma an kwashe su zuwa asibiti.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel