Tashin hankali: Yadda wani masifaffen Zakara ya kashe uwargijiyar sa har lahira

Tashin hankali: Yadda wani masifaffen Zakara ya kashe uwargijiyar sa har lahira

- Wani masifaffen zakara ya kashe wata mata har lahira a kasar Australiya

- Zakaran ya kai wa matar hari ne a lokacin da taje wajen da suke domin ta debo kwai

- Zakaran yayi ta cakun matar inda yayi sanadiyyar tsinka mata jijiyoyi, wanda yasa jini yayi ta zuba daga jikinta

Wata mata 'yar kasar Australiya ta rasa ranta sanadiyyar harin da wani masifaffen zakaranta ya kai mata.

A yadda rahoto ya nuna matar wacce ta dan kwana biyu a duniya ta shiga wajen kajin domin ta debo kwai sai kawai zakaran ya fara cakunta, inda ya tsinka mata jijiyoyin jikinta.

Sannan rahotannin sun kara bayyana cewa matar ta samu raunika da dama a jikinta amma babban dalilin da ya sa ta mutu shine jinin da ta dinga zubarwa daga jikinta.

KU KARANTA: Duniya ta zo karshe: An halatta aure tsakanin mutane da dabbobi a kasar Norway

Wannan daliline yasa aka fara fitar da gargadi akan dabbobin da idan ka gansu zaka yi tunanin basa yin komai amma kuma suna da babbar matsala.

Roger Byard Farfesa ne na jami'ar Adelaide dake kasar ta Australia, ya jima yana bincike akan irin matsalar da dabbobi za su iya kawowa mutane musamman ma tsofaffi.

Farfesan ya kara bayyana cewa wata mata ita ma ta mutu bayan mage (kyanwa) ta yagushe ta a kafa.

Ya kara da cewa ba wai iya harin da suke kaiwa tsofaffi mutane za su tsora da su ba, dabbobin suna da matsaloli da dama wadanda mutane ya kamata su lura da su da kyau.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel