Wani Matashi ya shiga hannu bisa laifin Luwadi da Yaro a jihar Katsina

Wani Matashi ya shiga hannu bisa laifin Luwadi da Yaro a jihar Katsina

Wata babbar kotun majistire a jihar Katsina, ta bayar da umarnin garkame wani matashi mai shekaru 35, Abubakar Bello a gidan kaso har zuwa ranar 8 ga watan Okotoba, biyo bayan tuhumarsa da laifin luwadi da ya aikata da wani saurayi mai shekaru 15 da ya kasance dan makwabcinsa.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, kotun bisa jagorancin Hajiya Fadila Dikko, ta bayar da umarnin ne a ranar Talatar da ta gabata kamar yadda jami'in dan sanda mai shigar da kara, Sergeant Lawal Bello ya nema.

A cewar jami'in dan sandan, wanda ake zargi da ya kasance mazaunin kauyen Daudawa a karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina, ya janye saurayin zuwa bayan gari daura da wani gulbi da ke kauyen Hayin Kado, inda ya aikata wannan mummunan ta'asa ta luwadi.

Bayan da mahaifin saurayin Hassan Adamu ya ankara da wannan lamari na mafi kololuwar kazanta da kuma duhu na zalunci, ya yi gagawar kai korafin hedikwatar 'yan sanda ta Faskari tun a ranar 8 ga watan Agustan 2019.

KARANTA KUMA: Tuna baya: Jaruman Arewa 5 da suka shiga dakin aure bara

A yayin da jami'in na sanda ya nemi karin lokaci a gaban kotun domin kammala bincike da gabatar da shaidu, babu shakka laifin da Abubakar ya aikata ya sabawa sashe na 284 na kundin tsarin dokokin kasa ta Penal Code.

A sanadiyar hakan ne kotun ta dage sauraron karar zuwa ranar 8 ga watan Oktoba inda za ta ci gaba da zamanta. Ta kuma bayar da umarnin a ci gaba garkame Abubakar a gidan dan Kande ba tare da bayar da izinin beli ba.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel