Hukuncin kotun zaben Kano bai shafi Dambazau ba – Jigon APC

Hukuncin kotun zaben Kano bai shafi Dambazau ba – Jigon APC

Wani jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki, ya soki hukuncin ranar Juma’a, 30 ga watan Agusta, da kotun zaben Kano ta yanke, inda ta soke zaben mamba mai wakiltan mazabar Sumaila/Takar a majalisar wakai, Hon. Shmasudeen Dambazau, kan hujjar cewa daga dan majalisar har jam’iyyarsa, babu mai shari’a a gaban kotun zaben.

Kotun zaben ta umurci hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da ta bayar da takardar shaidar cin zabe ga Surajo Kanawa, dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben.

Da yake martani ga hukuncin, jigon na APC wanda ya nemi a sakaya sunansa kan cewa ba a bashi umurnin magana da manema labarai ba kan lamarin, ya bayyana cewa jami’iyyar PDP ta gabatar da shari’a ne akan Abdulrahman Suleiman Kawu Ismaila amma ba wai akan Dambazau ba, inda yayi bayanin cewa tun farko wata babbar kotun tarayya ta yanke hukunci akan takarar Ismaila sannan ta umurci INEC da ta janye takardar shaidar cin zabensa sannan ta bayar dashi ga Dambazau.

Ya jadadda cewa ko kusa hukuncin bai da nasaba da Shamsudeen Dambazau, domin cewa babu inda aka ambaci sunansa a ko daya daga cikin takardun.

Jigon na APC ya shawarci Hon. Dambazau “da ya dauki mataki na gaba ta hanyar shirya tawagar lauyoyinsa don daukaka kara saboda rashin adalci ne kin sanar dashi cewa akwai wani shari’a a kotun zabe da ke gudana a matsayinsa na sahihin dan takarar APC.

KU KARANTA KUMA: Mutane 5 sun mutu yayinda motar tanka ta fashe a babban titin Kaduna zuwa Abuja

“Ina son ba magoya bayan Dambazau da matasan Najeiya baki daya tabbacin cewa babu wani abun damuwa game da lamarin sannan cewa tawagarsa na aiki tukuru domin tabbatar da cewar an kare masa hakkinsa. Don haka, kowa musamman al’umman mazabar Dambazau su kwantar da hankulansu. Ba zai bari a janye masa hankali ba sannan za a cimma duk wasu kudirori da yake shirin cimma a majalisar wakilai,” cewar jigon na APC.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel