Tirkashi: An bayyana wani birni a Najeriya da ya fi kowanne birni hadari a duniya
- An bayyana birnin Legas a matsayin birnin da yafi ko ina hadari a duniya
- Wata cibiya ce ta kasar Birtaniya ta gabatar da wannan bincike, inda a karshe ta gano birnin na Legas a matsayin birni mafi hadari a duniya
- Cibiyar ta gabatar da binciken akan birane guda sittin ne inda kuma birnin na Legas ya zo a na 56 da kuma 58 a bangaren rashin tsaro da rashin cigaba
Wani rahoto da cibiyar bincike akan tattalin arziki ta fitar ta bayyana garin Legas a matsayin garin da yafi kowanne gari hadari a duniya.
Cibiyar ta kasar Birtaniya wacca ta gabatar da binciken akan birane guda sittin na duniya, wajen yin la'akari da tsaro, lafiya, kayan more rayuwa da sauransu.
Cigaba ta bangaren cigaba a fannin abubuwan more rayuwa yana da mutukar muhimmanci wurin ingancin rayuwar mutane. Daya daga cikin wannan abubuwan shine samar da tsaro ga al'ummar yanki da 'yan kasuwa dama mutanen da suke shigowa domin ziyara.
KU KARANTA: To fah: Buhari bai taba zuwa makaranta ba a rayuwarsa, kuma duk takardun shi na bogi ne - Buba Galadima
Tokyo babban birnin kasar Japan shine birni na daya da aka bayyana wanda yafi ko ina zaman lafiya a duniya. Singapore, Osaka, Amsterdam da Sydney sune suka biyo bayan birnin na Tokyo. Wannan shine karo na farko da garin na Legas ya fito a cikin jerin biranen, sai dai kuma ya zo a matsayin 56 a bangaren matsalar tsaro, sannan kuma yazo na 58 a bangaren rashin cigaba.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng