Yadda wani bawan Allah ya shafe shekaru 36 a gidan kurkuku, saboda ya saci N18,000

Yadda wani bawan Allah ya shafe shekaru 36 a gidan kurkuku, saboda ya saci N18,000

- Wani mutumi ya shafe shekara 36 a gidan kurkuku saboda yayi sata a wani gidan biredi

- Mutumin mai suna Alvin Kennard yayi fashi da makami a wani gidan biredi, inda ya kwaci naira dubu goma sha takwas

- Wannan dalilin ne yasa aka yanke masa hukuncin daurin rai da rai, amma kuma wani alkali ya bayar da umarnin sakin shi a yanzu

An yanke hukuncin sakin wani mutumi daga gidan yari bayan ya shafe shekaru 36 a gidan yari saboda ya saci naira dubu goma sha takwas (N18,000).

Mutumin mai suna Alvin Kennard an yanke masa hukuncin kisa ne ba tare da beli ba, a lokacin tsohuwar dokar Alabama.

An kama Kennard yaje yin fashi da makami a wani gidan biredi, inda ya saci dala hamsin ($50), kimanin naira dubu goma sha takwas.

KU KARANTA: Tirkashi: An bayyana babban dalilin da yake kawo yawan 'yan luwadi da madigo a Najeriya

Tun lokacin mutumin mai shekaru 58 yake zaune a gidan kurkuku a matsayin hukuncin kisa. Sai dai kwatsam kuma wani alkali ya karbi rokon da yake yi masa inda ya bayar da umarnin a sake shi.

Yanzu haka dai alkalin kotun ya bayyana cewa yana cika wasu takardu ne domin aikawa gaba akan sakin Kennard.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng