Babu wanda ya mari Sanata Babba Kaita a garin Kankiya – Hadiminsa

Babu wanda ya mari Sanata Babba Kaita a garin Kankiya – Hadiminsa

Wani rahoton dake yawo a yanar gizo dake bayyana wasu matasa sun yi rikici da Sanata mai wakiltar mazabar Daura, Sanata Ahmad Babba Kaita ba gaskiya bane, kamar yadda wasu hadimansa suka tabbatar da Legit.ng.

A cikin makon nan ne Legit.ng ta wallafa wannan rahoto bayan samun bayanai daga wasu mazauna garin Kankiya inda aka ce rikicin ya auku, da suka hada da Malam Aminu da kuma wani Aliyu Maikudi daya wallafa a shafinsa na kafar sadarwar zamani ta Facebook.

KU KARANTA: Matsalar tsaro: Masari zai shiga cikin daji don tattaunawa da yan bindiga

Sai dai hadimin Sanatan a kan harkokin watsa labaru, Abdulkadir Lawal ya musanta aukuwar wannan lamari, inda yace babu kamshin gaskiya a cikin rahoton, asali ma wasu matasa ne suka yi kokarin cin zarafin Sanatan, inji shi.

Shima wani na hannun daman Sanata, Abbas Rimaye ya musanta rahoton cin zarafin Sanatan yayin da yake tattaunawa da jaridar Katsina Post, inda yace:

“Abin da ya faru shi ne wasu yan daba sun tare ayarin motocin Sanatan yayin wata ziyara daya kai mazabarsa inda suka nemi ya basu kudin kashewa, amma Sanatan ya yi birisa dasu. Babu shakka jama’a mazabar da Sanatan ya fito suna kaunarsa duba da gagarumar nasarar daya samu a zaben daya gabata.”

Daga karshe hadimin Sanatan ya yi kira ga jama’an yankin Daura, mutanen Katsina da ma al’ummar Najeriya gaba daya da su yi watsi da wannan rahoto, saboda a cewarsa babu wanda zai iya kawo hujjar hoto ko na bidiyo game da batun.

Shi dai Sanata Babba Kaita ya kasance tsohon dan majalisa ne dake wakiltar mazabar Kankia/Ingawa/Kusada a majalisar wakilan Najeriya tun daga shekarar 2011, sa’annan ya zama Sanata bayan rasuwar Sanatan yankin Daura, marigayi Mustapha Bukar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel