An yi garkuwa da awakin wani dan siyasa a kasar Habasha

An yi garkuwa da awakin wani dan siyasa a kasar Habasha

Kamar yadda jaridar BBC Hausa ta ruwaito, mun samu cewa, an yi awon gaba da garken awaki na wani dan siyasa a Kudancin kasar Habasha, a wani yunkuri na hana shi walwala ta ci gaba da harkokin siyasa a cewar shugaban jam'iyyar adawa ta Arena Tigray.

A cewar Abrha Desta, a ranar Larabar da ta gabata ne aka tarkace awakin guda 16 daga wata gona a garin Zenawi Asmelash daura da sansanin dakarun tsaro na Kola Temben a kasar da ke yankin Arewa maso Gabas a nahiyyar Afirka.

Kamar yadda Mista Desta ya bayyana, shugabannin jam'iyya mai mulki ta TPLF, a baya bayan nan sun kama dan siyasar mai sunan Mista Zenawi inda suka yi barazanar dagula masa duk wani lissafi na siyasa.

Ya zuwa yanzu sun kuma biyo ta hanyar yashe masa awaki a matsayin wata hanya ta muzguna wa rayuwarsa inji shugaban jam'iyyar adawa.

Babu shakka Arena Tigray kifaffiyar jam'iyyar adawa ce wadda ke ci gaba da kai ruwa rana na kara yawan 'ya'yanta domin daura damarar zaben da za a yi a shekara mai gabatowa.

Wannan lamari ya janyo ce-ce-ku-ce a zaurukan sada zumunta a kasar Habasha, bayan da Mista Abrha ya bayyana a shafin sa na Facebook cewa "jam'iyyar TPLF ta zama ta dabbobi ba mutane ba."

A yayin da ra'aoyoyi al'umma ke ci gaba da shan bam-bam, wasu sun mayar da lamarin tamkar abin raha a yayin da wasu suka nuna damuwa tare da bayar da muhimmanci da cewar zalunci ne kawai tsagwaransa.

KARANTA KUMA: Tinubu ya yi hasashen nasarar APC a zaben gwamnonin jihar Kogi da Bayelsa

Ba tare da bayar da wani cikakken bayani ba a yayin zantawa da manema labarai, shugaban 'yan sandan yankin ya tabbatar da aukuwar wannan lamari.

Hakazalika Mista Zenawi ya ce uku daga cikin awakin sun tsere daga inda aka tsare kuma tuni suka dawo gida, sai dai ana ci gaba da sanya idanu a kan sauran awaki 13 da aka yashe.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel