Innalillahi wa inna ilaihi raji’un: Yan bindiga sun yi awon gaba da Mata da yan mata 46 a Katsina

Innalillahi wa inna ilaihi raji’un: Yan bindiga sun yi awon gaba da Mata da yan mata 46 a Katsina

Wasu gungun yan bindiga dauke da muggan makamai sun kai farmaki a kauyen Wurma dake cikin karamar hukumar Dutsanma ta jahar Katsina inda suka kwashe tsawon sa’o’i uku suna cin karensu babu babbaka.

Legit.ng ta ruwaito wani Malamin jami’ar Umaru Musa Yar’adua, kuma dan asalin garin Wurma, Dikko Muhammad ne ya tabbatar da aukuwar mummunan lamarin a shafinsa na kafar sadarwar zamani ta Facebook.

KU KARANTA: Yan bindiga sun kai samame jahohin Katsina da Sakkwato, sun kashe 2 sun raunata 14

Dikko ya bayyana cewa yan bindigan sun yi awon gaba da mata da 'ya'yansu, masu ciki, masu goyo da kuma 'yan mata da yawansu ya kai mutane 46, ya kuma kara da cewa babu gidan dake garin Wurma da yan bindigan basu shiga sun yi ta’adi ba.

“Mun ga tashin hankali. Jiya tun qarfe 11:30pm ake harbe-harbe har 2:30am amma har na fito garin wajen 2pm babu wani jami'in tsaro ko na gwamnati da ya je in banda dan majalisar jiha. Babu Kwamishinan 'yan sanda, ba DPO, ba kowa.

“Kuma a haka wai cikin qasa muke da ake kira Najeriya! An dauki mata da 'ya'yansu; da masu ciki; da masu goyo; da 'yan mata- mutane arba'in da shida. Duk gidan da ke garin Wurma an bude shi, wani da takobi; wani da gatari; wani da bindiga.

“Duk abu mai amfani an dauke shi daga abinci zuwa sutura har takalma. Duk inda ke da babur tsakanin roba-roba da boxer da Jingcheng, duk sun dauke. Duk shagunan da ke garin sun fasa sun kwashe kayan; ko ashana babu ta sayarwa yau.

“Na ga yara 'yan shekara biyu da qasa da haka suna kukan rashin ganin iyayen su. Na ga abubuwan ban tausayi. Allah Ka tsare mana wadannan 'yan uwa na mu. Allah Ka kai masu dauki.” Inji shi.

A wani labarin kuma, wasu gungun yan bindigan na daban sun kai samame a wani kauye mai suna Shimfida dake cikin karamar hukumar Jibia ta jahar Katsina a ranar Lahadin data gabata, inda suka raunata wasu mata uku da harbin bindiga.

Baya ga nan yan bindigan sun kone wasu motoci guda uku kurmus mallakin Sojoji, da guda 1 mallakin hukumar Yansandan farin kaya, Nigeria Security and Civil Defence Corps. Yan bindigan sun tare hanya ne a daidai lokacin da yan kasuwa suke komawa gida bayan kammala cin kasuwar Shimfida.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel