Ya zama dole mutanen kirki su shiga cikin siyasa – Seyi Makinde

Ya zama dole mutanen kirki su shiga cikin siyasa – Seyi Makinde

Kamar yadda mu ka samu labari, Mai girma gwamnan jihar Oyo, Injiniya Seyi Makinde, ya yi kira ga mutanen kirki; maza da mata da su bazama cikin harkar siyasa domin su kawo gyara a kasa.

Gwamnan ya ce bai kamata mutanen Allah su rika gujewa siyasa ba inda ya ce idan a na samun mutanen kwarai a cikin tafiyar, sha’anin mulki zai gyaru kuma za a rika siyasa a cikin tsabta.

Seyi Makinde ya kuma kara da cewa siyasa ba za ta hana mutanen kirki masu gaskiya da amana shiga aljannar Ubangiji ba. Gwamnan ya yi wannan jawabi ne ta bakin Taiwo Adisa kwanan nan.

A wannan jawabi da ya fito daga ofishin Mista Taiwo Adisa wanda shi ne babban Sakataren yada labaran gwamnan, Seyi Makinde ya yi wannan kalamai ne a wajen wani biki da a ka shirya a coci.

An shirya wannan biki ne a babban cocin Katolika na St David wanda ke cikin babban birnin jihar Ondo na Akure domin nuna farin ciki game da nasarar da Makinde ya samu a zaben 2019.

KU KARANTA: Magu ya kai wani samame zuwa dakin karatun Obasanjo

‘Yanuwan gwamnan ta gefen Mahaifiyarsa ne su ka shirya masa wannan taron biki da addu’o’i inda Seyi Makinde ya ja hankalin Kiristoci masu gaskiya su shigo cikin harkar siyasa a kasar.

Gwamnan ya ke cewa: “Abin da wasu su ka dauka shi ne mutumin Allah ba zai taba shiga siyasa ba. Abin da a ke so shi ne mutum ya yi wa jama’a aiki cikin gaskiya tare da rike bautar Ubangiji.”

Mai girma gwamnan ya kuma cewa: “Yau zan bada labarin cewa na dare kan kujerar gwamna ba tare da ina da wani Ubangida a siyasa ba face Ubangiji na. Abin da wahala, amma aikin Allah ne.”

Makinde ya ce Iyayensa ba su yarda da shi ba da farko da ya shiga siyasa amma daga baya kowa ya ga zahiri. A karshe, gwamnan ya jawo ayoyi da kissoshi na yadda Ubangiji ya ke nuna ikonsa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel