Gwamnatin Jigawa ta ba da hutu ranar Talata

Gwamnatin Jigawa ta ba da hutu ranar Talata

Domin tunawa da shekaru 28 na samuwar jihar, gwamnatin Jigawa ta bai wa ma'aikatan ta hutu a ranar Talata, lamarin da ta ce su shakata kuma su yi wa jihar addu'o'i na samun aminci.

Sanarwar kaddamar da hutun ta zo ne a cikin wani sako da sa hannun kakakin ofishin shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar, Alhaji Isma'il Ibrahim, wanda ya gabatar yayin ganawa da manema labarai a ranar Litinin cikin birnin Dutse.

Ya ke cewa, "gwamnatin Jigawa tana taya dukkanin al'ummar jihar murnar zagayowar wannan rana, kuma tana fatan za su ribaci wannan lokaci wajen kwarara addu'o'i ga jihar da kuma kasa baki daya."

"A yayin haka kuma, gwamnatin jihar tana fatan dukkanin ma'aikata za su ribaci wannan lokaci na hutun kwana daya da suka samu wajen yi wa Allah godiyar wanzar da zaman lafiya a jihar da kuma ayyukan ci gaba na inganta jin dadin al'umma da gwamnatin jihar ke ci gaba da aiwatarwa."

"Kazalika gwamnatin tana jajantawa 'yan uwan wadanda suka riga mu gidan gaskiya da kuma sauran wadanda dukiyoyinsu suka salwanta a sanadiyar ambaliyar ruwa da ta auku a jihar da kuma wasu jihohi a kasar nan."

"Gwamnati tana fatan mutanen jihar mu za su ribaci kashedin da hukumomi masu ruwa da tsaki suka yi masu a kan hanyoyin dakile aukuwar ambaliyar ruwa a lokuta na gaba, inji Alhaji Isma'ila.

KARANTA KUMA: Zan wadata hukumar NITDA da kaifin basira - Kashifu Inuwa

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, ci gaba da saukar ruwan sama tamkar da bakin kwarya a wannan lokaci na damina, ya yi sanadiyar ambaliyar ruwa wadda ta ci fiye da gidaje 400 a jihar Jigawa, inda ta sanya daruruwan mutane suka kauracewa muhallansu.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel