Yaba kyauta tukwici: Sarkin Zaria ya baiwa Buhari kyautar ingarman doki

Yaba kyauta tukwici: Sarkin Zaria ya baiwa Buhari kyautar ingarman doki

Domin bayyana farin cikinsa, tare da godiyarsa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Dakta Shehu Idris ya baiwa shugaba Buhari kyautan wani ingarman doki.

Legit.ng ta ruwaito mai martaba Sarki ya mika wannan doki ne ga shugaban kasa Buhari hannu da hannu yayin da shugaba Buhari ya kai masa ziyara a fadarsa dake cikin birnin Zazzau domin gaisuwa da ban girma, a ranar Alhamis, 22 ga watan Agusta.

KU KARANTA: Madalla: Sojojin Najeriya sun bankado wani mugun shiri da Boko Haram ta yi a Borno

Yaba kyauta tukwici: Sarkin Zaria ya baiwa Buhari kyautar ingarman doki
Yaba kyauta tukwici: Sarkin Zaria ya baiwa Buhari kyautar ingarman doki
Asali: Facebook

Buhari ya samu rakiyar gwamnan jahar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai da kuma gwamnan babban bankin Najeriya, Mista Godwin Emefiele, tare da sauran jiga jigan jami’an gwamnatin jahar Kaduna da kuma masu rike da mukaman siyasa a jahar.

Idan za’a tuna shugaba Buhari ya kai ziyara aiki na yini daya garin Zaria domin kaddamar da wasu muhimman ayyuka da gwamnatin jahar Kaduna ta gudanar, da kuma wani aikin ciyar da ilimi gaba da babban bankin Najeriya ta yi.

Daga cikin manyan ayyukan da Buhari zai kaddamar a birnin Zazzau akwai:

Aikin samar da ruwan sha a garin Zariya wanda gwamnan jahar Kaduna, Nasir El-Rufai ya gudanar, idan za’a tuna, a shekarar 2017 aka kaddamar da kashin farko na aikin ruwan da a ke yi a Zariya. A yau kuma shugaba Buhari zai kaddamar da kashi na 2 na aikin, na samar da ruwa a yankin Sabon Gari da Zariya.

Aikin katafaren cibiyar ilimi ta “Center of Excellence” wanda babban bankin Najeriya CBN ta gina a cikin jami’ar Ahmadu Bello dake garin na Zariya

Sai kuma aikin madatsar ruwa ta Galma, Inda shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da wasu manyan tankunan ruwa da zasu dinga adana ruwa daya kai lita miliyan 150 don amfanin al’ummar Zariya da kewaye.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel