Ngige, Malami da sauran ministoci 10 da zasu maimaita mukamansu a zango na biyu

Ngige, Malami da sauran ministoci 10 da zasu maimaita mukamansu a zango na biyu

A wa'adin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari na biyu, ministoci 12 ne cikin 43 aka samu za su maimaita mukaman da suka rika a zango na farko. An rantsar da sabbin ministocin a ranar Laraba, 21 ga watan Agustan 2019.

Shugaban kasa Buhari a ranar Laraba cikin fadarsa ta Villa da ke birnin Abuja, ya rantsar da sabbin ministoci 43 da zasu jagoranci ma'aikatu a kasar inda kowanen su ya san makamar aikinsa.

Bayan sake dawowa karo na biyu, ministoci 12 ne aka samu za su maimata kujerun da suka jagoranta a wa'adin gwamnatin Buhari na farko. Ministoci tare da ma'aikatu gami jihohinsu sune kamar haka:

1. Anambra: Chris Ngige - Ministan Kwadago da samar da aiki

2. Ribas: Rotimi Amaechi - Ministan Sufuri

3. Katsina: Hadi Srika - Ministan Sufurin Jiragen Sama

4. Enugu: Geoffery Onyeama - Ministan harkokin kasashen ketare

5. Jigawa: Suleiman Adamu - Ministan Ruwa

6. Adamawa: Muhammad Musa Bello - Ministan Birnin Tarayya

7. Bauchi: Adamu Adamu - Ministan Ilimi

KARANTA KUMA: Sake kama Wadume za ta kore duk wani shakku - DHQ

8. Ebonyi: Ogbonnaya Onu - Ministan Kimiyya da Fasaha

9. Kaduna: Zainab Shamsuna Ahmed - Ministar Kudi

10. Kwara: Lai Muhammad - Ministan Labarai da Al'adu

11. Kebbi: Abubakar Malami - Ministan Shari'a

12. Legas: Babutunde Fashola - Ministan Ayyuka da Gidaje (Sai dai a yanzu an rage masa nauyin ma'aikatar makamashi).

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel