Yanzu Yanzu: Oyo-Ita ta yi zuwan bazata a Aso Rock

Yanzu Yanzu: Oyo-Ita ta yi zuwan bazata a Aso Rock

Shugaban ma’aikatan tarayya wacce ke tsaka mai wuya, Misi Winifred Oyo-Ita, a ranar Laraba, 21 ga watan Agusta ta yi bayyanar bazata a fadar Shugaban kasa da ke Abuja.

Fadar Shugaban kasa na shirin rantsar da sabon majalisa a yau Laraba.

Oyo-Ita ta isa fadar Shugaban kasa a cikin motarta na aiki kirar SUV da misalin karfe 9:45 na safe.

Kai tsaye ta wuce ofishin Shugaban ma’aikatan Shugaban kasa, Abba Kyari.

Tsawon kwanaki biyu bata halarci taron ministoci da Shugaban kasa ya shirya ba, wanda ya samu halartan manyan jami’an gwamnati.

Ku tuna cewa hukumar yaki da cin hanci da hana yi wa tattalin arziki zagon kasa (EFCC) a makon da ya gabata ta gasa Oyo-Ita akan zargin almundanan kwangilar naira biliyan 3.

KU KARANTA KUMA: EFCC ta zargi magoya bayan Ambode da yi wa jami’anta 3 rauni, da kuma lalata masu abun hawa

Rahotannin kafofin watsa laarai a ranar Litinin, sun yi ikirarin cewa Oyo-Ita ta gabatar da wasikar ajiye aiki.

Amma dai fadar Shugaban kasa ta bayyana cewa bata riga ta samu wasikar murabus din ba.

A wani labarin, Legit.ng ta rahoto cewa gabanin rantsar da sabbin ministocinsa yau, shugaba Muhammadu Buhari ya yi kira ga wadanda ya nada da suyi gaggawan samar da canji saboda shekaru hudu babu yawa kamar yadda ake tunani.

Amma gwamnoni 20 cikin 29 da aka rantsar rana daya da Buhari basu rantsar da nasu majalisar zantarwarsu ba.

A jiya Talata, 20 ga Agusta, Buhari ya yi jawabin a wajen kulle taron da aka shiryawa sabbin ministoci 43 da akayi a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel