Hankalin al’umman Ibbi ya kwanta bayan bazuwar labarin kama Wadume

Hankalin al’umman Ibbi ya kwanta bayan bazuwar labarin kama Wadume

Mataimakin kwamishinan yan sanda, Abba Kyari ya baro garin Ibbi a ranar Talata, 20 ga watan Agusta tare da motoci dauke da tarin kayan gona da aka kwato daga gidan gawurtaccen mai garkuwa da mutane, Hamisu Bala Wadume.

Wani majiya daga Ibbi wanda ya yi magana da majiyarmu ta DailyTrust ba tare da shakka ba yace Abba Kyari tare da tawagarsa sun tsallake tekun Benue a cikin jirgin ruwa da sanyin safiyar ranar Talata.

Majiyar yace har ila yau an ketara da motoci da kuma kayan gonan da aka gano a gidan madugun dan fashin ta Teku.

Ya bayyana cewa labarin kama Wadume ya zo wa al’umman Ibbi a matsayin abun kwanciyar hankali.

Yace Wadume yayi sanadiyyar bata sunan garin tare da bata martabar garin.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan Najeriya talakawa ne da ke fatan samun rayuwa mai kyau – Buhari ga ministoci

Daga karshe yace duk da cewar har yanzu akwai sauran jami'an sojoji da na yan sanda a garin, labarin kama Wadume ci gaba ne sosai sannan kuma zai kwantar da halin da aka shiga a lokacin farautar mai laifin.

Da farko dai mun ji cewa Hamisu Bala Wadume, rikakken mai garkuwa da mutane da jami'an 'yan sanda suka yi nasarar sake kama wa ranar Litinin ya bayyana yadda dakarun sojoji suka kubutar da shi daga hannun jami'an 'yan sanda na rundunar IRT (Intelligence Response Team) a ranar 6 ga watan Agusta.

Wadume ya kubuta daga hannun jami'an IRT ne bayan dakarun soji na bataliya ta 93 da ke Takum a jihar Taraba sun bude wa 'yan sandan da suka kama shi wuta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel