Bidiyo: Yadda sojoji suka budewa 'yan sanda wuta, suka kubutar da ni - Wadume

Bidiyo: Yadda sojoji suka budewa 'yan sanda wuta, suka kubutar da ni - Wadume

Hamisu Bala Wadume, rikakken mai garkuwa da mutane da jami'an 'yan sanda suka yi nasarar sake kama wa ranar Litinin ya bayyana yadda dakarun sojoji suka kubutar da shi daga hannun jami'an 'yan sanda na rundunar IRT (Intelligence Response Team) a ranar 6 ga watan Agusta.

Wadume ya kubuta daga hannun jami'an IRT ne bayan dakarun soji na bataliya ta 93 da ke Takum a jihar Taraba sun bude wa 'yan sandan da suka kama shi wuta.

Daga baya rundunar soji ta bayyana cewa dakarunta sun bude wa 'yan sandan wuta ne bisa kuskuren cewa 'yan ta'adda ne bayan an kira su tare da sanar da su cewa wasu mutane sun sace wani mutum.

'Yan sanda uku da wani farar hula ya mutu, yayin da wasu jami'an 'yan sanda biyar suka samu raunuka.

DUBA WANNAN: Sabon salo: Wadanda suka yi garkuwa da dan limami sun karbi giya a madadin kudin fansa

A sanarwar da Frank Mba, kakakin rundunar 'yan sanda na kasa, ya fitar ranar Talata, ya ce jami'an 'yan sanda sun sake kama Wadume a ranar Litinin, 19 ga watan Agusta.

A faifain bidiyon jawabinsa da rundunar 'yan sanda ta wallafa a shafinta na Tuwita ranar Talata, Wadume ya bayyana yadda sojoji suka kubutar da shi daga hannun jami'an IRT.

"Tabbas 'yan sanda sun kama ni, amma sojoji sun biyo su, sun bude musu wuta sannan sun kubutar da ni.

"Sojoji sun dauke ni zuwa barikinsu inda suka kwance ni, kuma suka sake ni.

"Bayan na koma gida ne sai jami'an 'yan sanda suka sake kama ni," a cewarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel