Sake kama Wadume za ta kore duk wani shakku - DHQ

Sake kama Wadume za ta kore duk wani shakku - DHQ

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce ta sake kama Alhaji Hamisu Bala wanda aka fi sani da Wadume, mutumin da hukumomin tsaron kasar ke zargi da jagorantar ta'adar garkuwa da mutane bayan kubucewarsa makonni biyu da suka gabata.

Wadume dai ya kubuce bayan da sojoji suka bude wuta kan jami'an 'yan sandan da suka kamo shi a karo na farko, lamarin da ya gadar da zaman doya da manja tsakanin rundunar soji da kuma ta 'yan sanda a kasar.

A ranar 6 ga watan Agusta ne 'yan sandan Najeriya suka yi nasarar kama Wadume a jihar Taraba, amma ya kubuce a yayin da suke yunkurin mika shi babban ofishinsu da ke birnin Jalingo a sanadiyar bude masu wuta da wasu dakarun soji suka yi har lahira.

A daren ranar Litinin da ta gabata ne rundunar 'yan sandan Najeriya ta sanar da sake cafke Wadume cikin wani gida a layin Allo na unuwar Hotoro a jihar Kano inda kuma ta garzaya da shi babban ofishinta na kasa.

Bayan da ya tabbatar da shigarsa hannu, Wadume ya labartawa mahukunta tare da manema labarai tabbacin sa'insar da ta auku tsakanin wasu sojoji da ke tsaron hanya da kuma 'yan sandan wadda ta kai ga budewa tawagar 'yan sandan wuta da ta jagoranci cafke shi.

KARANTA KUMA: Ya kamata gwamnati ta bai wa Almajiranci kulawa - Ganduje

Sai dai biyo bayan wannan lamari, wani babban jami'in tsaro da ya bukaci a sakaya sunansa daga babban ofishin hukumar tsaro ta kasa DHQ da ke garin Abuja, ya ce sake cafke Wadume ya zuwa yanzu za ta kore duk wani shakku da rade-radin da ke yaduwa a kan harkallar.

Ya ce sannu a hankali duk wani shakku da rashin tabbas zai kau a yayin da Wadume ya fara bayani na bayar da shaidar yadda ta kasance, lamarin da a baya ya nemi hada 'yan sanda da sojojin kasar fada.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel