Da duminsa: Zan fito takarar gwamnan jihar Kano a 2023 - Nazir M Ahmad (Sarkin Waka)

Da duminsa: Zan fito takarar gwamnan jihar Kano a 2023 - Nazir M Ahmad (Sarkin Waka)

- Fitaccen mawakin nan na jihar Kano wanda Sarki Muhammadu Sanusi ya yiwa sarautar Sarkin Waka wato Nazir M Ahmad ya fito ya bayyana wani kudurinsa

- Fitaccen mawakin ya fito ya bayyana cewa zai fito takarar gwamnan jihar Kano a shekarar 2023 idan Allah ya kaimu

- Sai dai kuma mawakin bai bayyana ko a wacce jam'iyya yake da shirin fitowa takarar ba, yayin da yake bayanin hakan a shafinsa na Instagram

Majiyar jaridar Najeriya Hausa ta shafin Facebook, ta bakin wakilinta Ibrahim Musa Tiyagas dake jihar Kano ta bayyana cewa, shahararren mawakin nan na jihar Kano, wanda kuma Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu ya bai wa sarautar Sarkin waka wato Nazir M Ahmad, ya sha alwashin fitowa takarar kujerar gwamna a jihar Kano a shekarar 2023.

Sai dai kuma shahararen mawakin Nazir M Ahmad, bai bayyana ko a wacce jam'iyya yake da shirin fitowa takarar ba.

KU KARANTA: Tirkashi: Jarumar Indiya ta wulakanta jarumi Sarki Ali Nuhu

Bugu daa kari fitaccen mawakin ya bayyana wannan aniyar ta shi ta tsaya takarar gwamnan jihar ta Kano a shafinsa na Instagram, a inda yayi bayani a cikin wani bidiyo tare da kuma bayyana ra'ayinsa.

Idan ba a manta ba satin da ya gabata mun kawo muku rahoton yadda gwamnatin jihar Kano ta kama babban daraktan masana'antar Kannywood Sunusi Oscar 442, inda wannan kamashi din ya dinga karawa sama hazo a shafukan sada zumunta.

Sannan kuma wannan kamashi din da aka yi yaso raba kan kungiyar fina-finan Hausan ta Kannywood, inda wasu ke ganin an sanya munafurci a lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel