Adam A Zango ya daura damarar lalata tarbiyyar 'yammata Musulmai na arewa - Datti Assalafiy
- Idan ba a manta ba kwanakin baya Adam A Zango ya fitar da sanarwa cewa ya fita daga kungiyar Kannywood saboda kama abokinsa daraktan shirya fina-finai OSCAR
- Yanzu yana so zai ci gashin kanshi, tun daga ranar da ya bayyana ficewar tasa ya fara neman hanyar da zai hada tashi kungiyar
Wannan dalilin ne yasa fitaccen mai akidar addinin Musuluncin nan ya gabatar da bincike akan lamarin, inda ya bayyana cewa wannan magana ta jarumin ba haka take ba, inda ya ce:
"Babban dalilin da yasa Adam A Zango ya fice daga Kannywood ba don an kama OSCAR bane, dalilin shine ya tanadi wasu shirye shirye na iskanci da badala a cikin fim da waka da rawa na fitsara da rashin albarka, yana so ya fitar da su kasuwa, amma tsoron kamun hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ya hanashi fitarwa.
"To shine bayan an kama OSCAR sai yayi amfani da wannan damar yace ya fita daga cikin kungiyar Kannywood don ya samu ikon yada fasadi da barna a tsakanin Musulmi, Billahi munyi wannan binciken har daga abokan harkansa na kusa da suka san sirrinsa ciki da bai.
"Muna kan nazari a haka, kwatsam sai dazu mukaci karo da sanarwan da Adam A Zango ya fitar cikin bidiyo a shafinsa na Instagram yana mai cewa; yana neman 'yan mata kyawawa danyu shakaf wadanda suke tashen balaga 'yan kasa da shekarun haihuwa 18, yana so zai sakasu a fim, ya kuma bukaci duk wacce take bukata ta saka hotonta da dukkan bayananta.
"A ka'idah wannan tsarin da Adam A Zango ya fitar ya karya kowace irin doka ta shirya fina-finai a Kasarmu Nigeria, sannan sai muka fahimci wannan wata hanyace da yake so yabi domin ya cimma wani buri nashi, ayi kasuwanci da 'ya'yan mutane a kuma lalata musu tarbiyyah da rayuwa.
"Amma zamu tura 'yan leken asirinmu daga cikin irin 'yan mata da yace yana so Insha Allah, kuma hakkin gwamnatin jihar Kaduna ne ta saka ido akan abinda Adam A Zango ya ke so yayi da 'ya'yan mutane, na kusa da Maigirma gwamnan Jihar Kaduna ku tayamu isar da wannan sakon.
KU KARANTA: To fah: Aisha Idris karuwa ce aka bata kudi dan ta batawa Ali Nuhu da Afakallahu suna - Jarumi Aminu Ahlan
"Ke kuma 'yan mata, ki sani gurin da zaki guri ne da za'a lalata miki darajar rayuwa na har abada, mutuncinki da darajar da Allah Ya miki ya kamata ki kebanceshi ga mijinki na aure uban 'ya'yanki na halal, ki sani gurin da zaki je, guri ne da za'a koya miki mummunan sana'a
"Abinda yake so yayi shine, duk 'yan matan da suka cika wannan fam da ya fitar ta yanar gizo-gizo suka saka hotunansu, to daya bayan daya za'a dinga kiran 'yan matan ace su zo a tantancesu, idan an gama da ita an lalata mata rayuwa sai a kira wata sabuwa, tunda ba abune da za'a hadu a guri daya a tantancen 'yan matan ba, ta yanar gizo-gizo ne ya fitar saboda mummunan manufarsa.
"Muna kira ga iyaye su saka ido akan 'ya'yansu 'yan mata.
"Adam A Zango kaji tsoron Allah, Ka tuna zaka mutu watarana, ka tuna daga cikin abokan sana'arka sun mutu, kai ma fa zakaje inda suka je, akwai hisabi, ina jiye maka tsoron ranar da zakayi nadama marar amfani, idan kayi sanadiyyar lalata rayuwar wani ko wata tamkar ka lalata rayuwar al'umma ne gaba daya, haka idan kayi sanadin shiryar da wani ko wata kamar ka shiryar da al'umma gaba daya, lada ko zunubinka kenan a gurin Allah.
"Idan ba zaka tuba ba, to ina mai tabbatar maka ba zakaci nasara ba, domin zamu kira al'ummar Musulmi, mu saka goshin mu a kasa mu kai karanka gurin Allah Madaukakin Sarki.
"Ina rokon Allah Ya shiryar da kai tare da masu mummunan sana'a irin taka, idan ba zaka shiryu ba muna tawassuli da Sunayen Allah AL-HAYYU, AL-QAYYUM ya mana maganinka cikin sauki Amin."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng