Muna fuskantar kalubale na yawan jama'a a Najeriya - Buhari

Muna fuskantar kalubale na yawan jama'a a Najeriya - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin, ya bayyana fargabarsa kan yadda adadin al'ummar Najeriya ke ci gaba da karuwa babu kakkautawa, lamarin da ya ce yana matukar razanar da shi.

Ya nemi zababbun ministocinsa da su hannu-da-hannu da juna wajen tunkarar duk wani kalubale da ya tunkaro kasar a yanzu. Ya nemi da su tabbatar da hadin kai a tsakanin su domin cimma manufofin gwamnati.

Furucin shugaban kasar ya zo ne yayin gabatar da jawabai a wani taron kwanaki biyu na musamman da aka fara gudanarwa a garin Abuja tare da zababbun ministocinsa da kuma manyan kusoshin gwamnati.

Da yake zayyana jawaban yayin taron da aka gudanar a fadarsa ta Aso Villa, shugaban kasar ya ce Najeriya tana fuskantar kalubale na yawan jama'a a yayin da adadin al'ummar kasar nan ya kusa kai wa mutum miliyan 200.

Ya hikaito alkalumman Majalisar Dinkin Duniya UN wadda ta yi hasashen cewa zuwa shekarar 2050, Najeriya za ta kasance kasa ta uku a duniya ta fuskar yawan mutane, wanda ta kiyasta cewa mutanen kasar za su iya kai wa mutum miliyan 411.

KARANTA KUMA: Buhari ya san masu tayar da zaune a Najeriya - Falana

Ko shakka babu shugaban kasar ya ce yawan jama'a zai zamto wata babbar damuwa a Najeriya muddin muka ci gaba da zama jiran taimakon kasashen duniya da suka kasaita. Ya nemi sabbin ministoci da su dukufa wajen shimfida tubalin da sai sanya kasar nan kan tafarki na ci gaba.

Cikin bugun baga, shugaba Buhari ya bayyana yadda gwamnatinsa a wa'adi na farko ta yi gagarumar nasarar wajen inganta tsaro, bunkasa tattalin arziki da kuma yaki da rashawa, lamari da ya ce masu adawa da 'yan hana ruwa gudu ne kadai za su musanta.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel