Sabbin Dokoki 11 da aka shimfida kan sha'anin aure da zanen suna a jihar Kebbi

Sabbin Dokoki 11 da aka shimfida kan sha'anin aure da zanen suna a jihar Kebbi

Cikin wata rubutacciyar takarda da ta fito daga fadar mai martaba Bahindin Bugudo na karamar hukumar Bagudo ta jihar Kebbi, Alhaji Muhammad Sambo Kaliel, an shimfida sabbin dokoki ga al'ummar gudunmar kan sha'anin aure da zanen suna.

Bayan farawa da sunan Allah mai rahama mai jin kai, takardar mai dauke da kwanan watan ranar 19 ga watan Agustan 2019, ta bayyana sanarwar dokokin da gudunmar Bahindin Bagudo ta shata bisa sha'anin aure da zanen suna.

Kamar yadda rubutun takardar ya bayyana, "mu mutanen kasar Bahindin Bagudo, mun zauna mun shata dokokin da suka shafi sha'anin aure da zanen suna domin saukakawa jama'armu wahalhalu bisa ga sunnar Annabi Muhammad (S.A.W)."

Dokokin sune kamar haka:

1. Shiga Gida: Kwandon Goro daya da naira dubu biyar (N5,000).

2. Hira: Mai bidar yarinya aure ba zai hira da ita da daddare ba sai dai da rana.

3. Kwaryar Sallah, Kayan Sallah da Kayan Shayi: Doka ta soke wannan abubuwa da ake yi.

4. Sadaki: Sadaki kada ya yi kasa da rubu'in dinari akalla, amma ba ya da iyaka.

5. D.J: Doka ta hana yin D.J wurin bikin aure da zanen suna.

6. Kida: Doka ta soke yin kidi da roko wajen bikin aure da zanen suna.

7. Gara: Doka ta hana yin gara, amma ana raka amaryar da buhu hudu na abinci da kayan miya.

8. Yinin Biki: Doka ta yarda Mata su je wurin yinin biki, amma an hana kidi da D.J waejn biki.

9. Wankin Amarya: Doka ta hana wankin amarya waje, sai dai cikin gidan mahaifinta.

10. Rali: Doka ta soke yin Rali.

11. Picknic: Doka ta hana yin Picknic.

KARANTA KUMA: An canza wa wata Mata hanci a Ingila

Legit.ng ta fahimci, baya ga kadd-kade da kuma raye-raye a wurin biki, rali wato zagaye a kan ababen hawa ya haramta a sabbin dokokin da masarautar Bahindin Bagudo ta shata. Haka zalika, Picknic, wato fita yin tantande da makulashe a wuraren shakatawa sun haramta a sabbin dokokin da aka fitar.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel