Yan Shi’a sun sha alwashin dawo da zanga-zanga, sun nemi sanin inda El-Zakzaky yake

Yan Shi’a sun sha alwashin dawo da zanga-zanga, sun nemi sanin inda El-Zakzaky yake

Mabiya kungiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN), wacce aka fi sani da Shi’a, sun sha alwashin dawo da zanga-zangarta na yau da kullun a kasar, sakamakon takunkumin da gwamnatin Najeriya ta sanya wa shugabansu, Sheikh Ibahim El-Zakzaky bayan ya je kasar Indiya yin magani.

Kungiyar ta kuma yi Allah wadai da yadda aka yi wa Shugaban nasu da kuma tafiya dashi da jami’an DSS suka yi, a lokacin da ya isa filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe International Airport, Abuja, zuwa wani wuri da ba a sani ba a ranar Juma’a, 16 ga watan Agusta.

A wani jawabi dauke da sa hannun kakakin kungiyar, Ibrahim Musa, mabiya El-Zakzaky sun bayyana cewa za su ci gaba da zanga-zangarsu domin tursasa gwamnati bin umurin kotun Kaduna da ta bukaci a sake shi domin zuwa yin magani.

Kungiyar ta bayyana cewa mahukuntan Najeriya sun nuna cewa hankalinsu bai kwanta da damar da aka ba shugabansu na zuwa neman magani a wajen kasar ba.

KU KARANTA KUMA: Ahmad Lawan ya jagoranci shugabannin majalisar dattawa zuwa wajen Buhari a Daura

A baya mun ji cewa kungiyar Shia ta Najeriya, IMN, ta zargi gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da kokarin halaka shugabanta, Ibrahim Zakzaky yayin da ya tafi jinya a kasar Iran ne, inji rahoton jaridar Daily Nigerian.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Kaakakin kungiyar, Ibrahim Musa ne ya bayyana haka a ranar Juma’a, inda yace gwamnatin ta yi kokarin yin amfani da kawayenta na kasashen waje ne wajen kashe Zakzaky a Indiya, amma suka gano.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel