Abubuwa 10 da ya kamata ku sani dangane da sabuwar dokar gidajen yari

Abubuwa 10 da ya kamata ku sani dangane da sabuwar dokar gidajen yari

A ranar Laraba, 14 ga watan Agusta, ne dai Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a kan dokar sauya tsarin gidan yari. Hakan ya haifar da canja wa hukumar ta gidajen yari suna, zuwa hukumar gidajen gyara halayen ‘yan Najeriya.

Saboda haka ne muka tattaro abubuwan lura guda goma akan haka wadanda suka hada da:

1. Sauya sunan Hukumar daga Nigerian Prisons Service zuwa Nigerian Correctional Service.

2. Tun cikin watan Janairu, 2008 ne Sanata Victor Ndoma-Egba ya gabatar da kudirin lokacin ya na sanata, sai dai kuma hakan bai yiwu a sai a shekaranjiya Laraba aka sanya masa hannu ya zama doka.

3. Wannan sabuwar doka ta bai wa Shugaban Kula da Gidajen yari na kowace jiha ikon kin karbar karin daurarru daga kotu, matukar gidajen kurkukun da ke jihar sun rigada sun cika da mutane.

4. An raba aikin ma’aikatan gidan kurkuku zuwa bangare biyu. Akwai bangare na farko shi ne na ‘Custodian’ sai na biyu kuma ‘Non-custodian.

5. Custodian za su rika kula da batutuwa da kula da wadanda aka tsare tare da tabbatar da an killace su a wuri ba wulakantacce wanda bai kamata a ajiye mutum ba. Su ne kuma za su kula da ganin cewa an rika gaggauta yanke wa wadanda ke jiran hukunci hukuncin su a kan lokaci.

6. ‘Non-custodian kuma za su maida hankali ne a kan ayyukan yau da kullum na ofis da sauran aikace-aikacen ayyukan da ake sa daurarru na ladabtarwa da duk wani hukuncin da kotu ta yanke a zartas kan wanda ta tsare.

7. Manufar doka da oda shi ne a maida hankali kan gyara halayya da dabi’un mutane, saita wa kangararru kwakwalwa da alkiblar rayuwa da kuma sake karbar su a cikin al’umma bayan sun canja halaye sun zama nagari.

8. Daga yanzu Shugaban Hukumar zai kasance ya na da Mataimaka har guda takwas, a matsayin sa na Kwanturola Janar.

9. Za a kirkiro da tsarin saisaita alkibla da dabi’un wadanda ke tsare, ta hanyar kulawa da lafiyar su, da hankulan su, ba su shawarwari da yi musu nasihohi da wa’azi. Za a rika gudanar da wadannan har ga manyan masu laifi tuburan.

KU KARANA KUMA: Yanzu Yanzu: Jami’an DSS sun tasa keyar El-Zakzaky a lokacin da ya dawo Najeriya

10. Idan wanda kotu ta yanke wa hukuncin kisa ya shafe shekara goma ya na jekala-jekalar daukaka kara, amma bai yi nasara ba, kuma har lokacin ba a zartas da hukuncin kisan a kan sa an kashe shi ba, to Babban alkali zai iya yi masa sasauci ya maida hukuncin sa daga na kisa zuwa daurin rai-da-rai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel