Tashin hankali: Tsananin talauci da yunwa yasa na taba cin kashin mutum - In ji wata mawakiya

Tashin hankali: Tsananin talauci da yunwa yasa na taba cin kashin mutum - In ji wata mawakiya

- Wata fitacciyar mawakiya 'yar kasar Ghana ta bayyana yadda rayuwa ta kasance a wajenta lokacin da tana karama

- Mawakiyar ta bayyana cewa ta taba cin kashin jariri saboda ta samu ta rayu

- Ta ce lokacin da tana karama ta taso cikin matsanancin talauci da yunwa, inda har ta kai ta ga cin kashin mutum saboda kada yunwa ta kasheta

Fitacciyar mawakiyar cocin nan 'yar kasar Ghana, Celestine Donkor ta bayyanairin wahalar da ta sha a rayuwarta a lokacin da take yarinya.

A cewar fitacciyar mawakiyar, ta taso a cikin bakin talauci, inda dalilin hakan yasa ta taci kashin mutum saboda ta samu ta rayu.

KU KARANTA: Bidiyo: Aisha Idris ta tona asirin shugaban hukumar tace fina-finan Hausa da yadda ya so yayi zina da ita

Mawakiyar ta bayyana yadda lamarin na ta ya faru kamar haka:

"Wata rana na taba zuwa wani gida domin na karbi abinci, sai na iske mai gidan bayanan. Mai aikin gidan ya umarceni da dole sai na ci kashin jaririn gidan kafin ya bani abincin da zanci."

Mawakiyar ta bayyana cewa a lokacin ba ta da wani zabi da ya wuce ta ci wannan kashi, saboda tana mutukar jin yunwa a lokacin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel