Bidiyo: Aisha Idris ta tona asirin shugaban hukumar tace fina-finan Hausa da yadda ya so yayi zina da ita

Bidiyo: Aisha Idris ta tona asirin shugaban hukumar tace fina-finan Hausa da yadda ya so yayi zina da ita

- A wannan karon Aisha Idris ta fedewa shugaban hukumar tace fina-finan Hausa biri har wutsiya

- Inda ta dinga tsine mishi tana cewa duk duniya ba ta taba ganin dan iska irinshi ba

- Ta ce da hannunsa ya sha tura mata hotunansa a otel idan kuma ya karyata za ta sanya a shafinta na Instagram duniya ta gani

A wani sabon bidiyo da ta yi ta wallafa a shafinta na Instagram, Aisha Idris dake zama a kasar Germany, wacce kuma ta yi wani bidiyo take tsinewa fitaccen jarumi Ali Nuhu akan cewa shi munafiki ne, yau ma ta kara zuwa da wani sabon bidiyo, inda ta fede biri har wutsiya akan shugaban hukumar tace fina-finan Hausa na Kannywood.

Aisha ta tonawa shugaban asiri inda ta bayyana cewa ya san ko ita wacece, kuma ta san duka iskancin da yake tsulawa a masana'antar Kannywood, sannan ta yi masa barazanar cewa idan har yana da ja ya fito yayi magana ita kuma tana da shaidu da hujjoji da za ta sanya a shafukan sada zumunta da za su tabbatar da abinda ta fada gaskiyane.

KU KARANTA: To fah: Shugaba Buhari ya ce zai kawo karshen talauci a Najeriya, yayin da kuma ya bayyana bangaren da zai ba wa muhimmanci a wannan karon

Ga maganar da Aisha Idris ta yi a cikin bidiyon:

"A wannan karon zanyi magana ne akan Afakallahu, kuma kai ka sanni da kyau ni ba bakuwa bace a wajenka saboda gaskiya tana da daci, kai yanzu har su Ali Nuhu ne za su dinga zugaka ka dinga yin wasu abubuwa saboda kuna tafiya da gwamna kuna cewa ku Khadimul Islam ne, akwai dan iska irinka ne.

"Ka fito ka karyata ni idan karya nake maka, ka san kana karyata ni akwai abubuwan da zan saka a shafin Instagram duniya ta gani kowa ya san wanene kai.

"Tunda nake ban taba ganin dan iska ba a masana'antar Kannywood kamar ka, kowa ya san wannan a Kannywood sunyi shiru ne kawai saboda suna tsoron ka.

"Ina kira ga 'yan Kannywood da ku daina girmama mutane 'yan iska irinsu Afakallahu, ku daina kiranshi shugaba, ku mutane ne masu 'yanci, dan iska ne wallahi, saboda ya sha yi mini maganar iskanci, idan kuma ya ce karya ne zan sanya a kafar sada zumunta duniya ta gani.

"Duk Kannywood babu mai zunubi irinka, tunda bin yaran mutane kake yi kana lalatawa kowa ka gani kace kana so, kawai idan kaga mace tunaninka 'yar iskace, baka san tana da aure ba ko babu, kai dai kawai burinka ka samu kayi lalata da mace shikenan hankalinka ya kwanta.

"Ka tura mini da lambarka kace mini na nemeka, nayi maka magana a WhatsApp, kace mini kaine shugaban fim din Hausa, ban sanka ba saboda bani da alaka da fim din Kannywood, ni kawai ina kalla ne saboda yana burgeni.

"Kada ka mance ka tura mini da hotunanka a otel sunfi guda goma ina da su a cikin wayana, saboda kayi tunanin nima 'yar iska ce, amma wai har kaine kake sawa a kama Sunusi Oscar, akwai tsinanne irinka a Kannywood ne.

Ku kalli bidiyon a kasa:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel