Sabuwar dokar Buhari a kan kayan abinci za ta kara jefa 'yan Najeriya cikin tsananin yunwa - PDP

Sabuwar dokar Buhari a kan kayan abinci za ta kara jefa 'yan Najeriya cikin tsananin yunwa - PDP

Jam'iyyar PDP ta bayyana cewa sabon umarnin da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayar a kan janye tallafi a kan shigo da kayan abinci ya zo a lokacin da bai dace ba, musamman idan aka yi la'akari da halin kuncin rayuwa da 'yan Najeriya ke ciki.

A ranar Talata ne Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa ya umarci babban bankin kasa (CBN) da ya daina bayar da tallafin canjin kudi ga masu kasuwancin shigo da abinci cikin Najeriya.

A wani jawabi Garba Shehu, kakakin shugaba Buhari, ya fitar, ya ce shugaban kasa ya bayar da wannan umarni ne domin inganta cinikin kayan abincin da aka noma a cikin gida.

Da yake karbar bakuncin manyan 'ya'yan jam'iyyar APC a gidansa na garin Daura, shugaba Buhari ya ce gwamnati zata yi amfani da kudin tallafa wa masu shigo da kayan abinci wajen inganta tattalin arziki.

DUBA WANNA: Dawowa Najeriya: Dalilai 6 da suka sa Zakzaky barin kasar Indiya ba shiri

Amma, a cikin wani jawabi da sakatarenta na yada labarai, Kola Ologbondiyan, ya fitar a ranar Alhamis, PDP ta ce sabon umarnin na Buhari zai, "zai kawo lalacewar ingancin abincin da jama'a zasu ke ci, sannan kuma ya kara jefa kasa cikin halin tsananin, bayan wanda ake fama da shi."

Ya kara da cewa gwamnatin jam'iyyar APC ta kara tabbatar da cewa, "ba ta tausayin halin kunci, fatara da yunwar da miliyoyin 'yan Najeriya ke ciki, suna kokarin kara saka kayan abinci ya kara tsada fiye da yadda suka janyo tsadarsu bayan zuwa ofis a shekarar 2015.

"Abin takaice ne a ce sabanin gwamnati ta kawo wa jama'a sauki, shugaba Buhari ya bayar da umarni cire dukkan wani tallafi a kan kayan abincin da ake shigo da su Najeriya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel