Tattalin arziki: Buhari bai san inda a ka dosa ba – Inji Oby Ezekwesili

Tattalin arziki: Buhari bai san inda a ka dosa ba – Inji Oby Ezekwesili

Oby Ezekwesili wanda ta rike mukamin Ministar ilmi da ma’adanan Najeriya a gwamnatin Olusegun Obasanjo ta soki tsarin tattalin arzikin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Madam Oby Ezekwesili ta bayyana cewa matakin da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauka na daina bada Daloli ga ‘yan kasuwa domin shigo da abinci daga kasar waje.

A cewar Oby Ezekwesili, shugaba Buhari bai san halin da kasar nan ta ke ciki ba. Tsohuwar ‘yar takarar shugaban kasar ta yi amfani da shafin ta na Tuwita wajen sukar wannan danyen mataki.

Ezekwesili ta ce “Duk da mun san cewa Buhari mutum ne wanda bai damu da alkaluma ba, amma za mu dauki lokaci mu yi bayanin abubuwan da ya kamata a ce Buhari la’akari da su tun farko.”

KU KARANTA: Matakin da Shugaba Buhari ya dauka ya jawo masa yabon Shehu Sani

Tsohuwar Ministar ta Najeriya ta ke cewa kamata ya yi a ce shugaban kasar ya duba wadannan alkaluman tattalin arzikin na ta kafin ya yi gigin kataborar da ya yi na hana shigo da abinci.

Bayan nan kuma Madam Ezekwesili ta nuna cewa bai kamata a ce shugaban kasa ba ne zai rika fadawa babban bankin Najeriya na CBN abin da zai yi domin kuwa bankin na da cikakken ‘yanci.

Babbar Masaniyar wanda ta yi aiki a babban bankin Duniya ta jero wadannan alkaluma a shafin na ta na Tuwita ta na mai cewa fadanci kurum shugaban kasar ya sa a gaba ba shugabanci ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel