Tashin hankali: Wuta ta babbake wani magidanci a dakin budurwarsa

Tashin hankali: Wuta ta babbake wani magidanci a dakin budurwarsa

An bayyana cewa wutar gobara ta babbake wani magidanci a gidansa da ke yankin Oginigba Transamadi a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas.

Magidanci, wanda aka ce direban jirgin ruwa ne, ya mutu ne sakamakon tashin gobara a lokacin da yake shakata wa a dakin burwarsa ranar 10 ga watan Augusta.

Wani ma'abocin amfani da dandalin sada zumunta, Victor James, ne ya sanar da mutuwar mutumin a shafinsa na 'Facebook' ranar 12 ga watan Augusta.

"Gobara ta babbake wani magidanci a dakin budurwarsa da ke yankin Trans Amadi a garin Fatakwal, ranar 10 ga watan Agusta. Duk matar da ta san mijinta direban jirgin ruwa ne kuma bai dawo gida ba, sai ta ziyarci ofishin hukuma na yankin," kamar yadda James ya wallafa a shafinsa na 'Facebook'

DUBA WANNAN: Miji, mata da 'ya'yansu biyu sun mutu bayan cin abincin Sallah a Kebbi

Jama'a da dama sun bayyana mabanbantan ra'ayi a kan faruwar lamarin.

A yayin da wasu ke tausaya wa magidancin, wasu shawara suke bawa masu aure da su tsaya ga matansu ko don gudun saka kansu cikin hatsari da bata sunansu da na iyalinsu a idon jama'a.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel