Gwamnan jahar Borno ya sake nada wasu mutane 11 muhimman mukamai a gwamnatinsa

Gwamnan jahar Borno ya sake nada wasu mutane 11 muhimman mukamai a gwamnatinsa

Gwamnan jahar Borno, Farfesa Babangana Umara Zulum ya amince da nadin wani tsohon Soja, Kanal A.A Chiroma mai ritaya a matsayin mai bashi shawara a kan harkokin tsaro, inji rahoton kamfanin dillancin labarum Najeriya, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kaakakin gwamnan, Malam Isa Gusau ne ya sanar da haka a ranar Laraba, 14 ga watan Agusta, inda ya kara da cewa gwamnan ya amince da nadin Kanal Chiroma tare da sauran mutane 10 don kasancewa manyan hadimansa.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari ta sauya sunan hukumar kula da gidajen yarin Najeriya

Isa Gusau ya bada tabbacin dukkanin mukaman suna da matukar muhimmanci, kuma guda biyu daga cikinsu zasu yi aiki ne a ofishin mataimakin gwamnan jahar, haka zalika yace gwamnan zai sanar da ranar da zai rantsar dasu, amma dai nadin nasu ya fara ne nan take.

Sauran sabbin manyan hadimai guda 10 sun hada da:

Malam Ali Jato, hadimin gwamna a kan harkokin ayyuka a Abuja

Christopher Akaba, hadimin gwamna a kan samar da ayyuka da tallafa ma matasa

Sale Habib, hadimin gwamna a kan taruka da tsara lokaci

Malam Bukar Mustapha, hadimin gwamna a kan tattara da adanar bayanai

Mustapha Bulu, hadimin gwamna a kan tafiyar da kudaden al’umma

Yusuf Shettima, hadimin gwamna a kan sanya idanu a kan manyan ayyuka

Malam Abdullahi Yusuf, hadimin gwamna a kan tattara bayanan manyan ayyuka

Sai kuma Shuaibu Adamu da Alfred Bwala a matsayin mataimaka na musamman a ofishin mataimakin gwamna.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel