Ka aure ni ko na kashe kaina - Bidiyon Budurwar da ta dinga suma tana rokar saurayinta ya aureta

Ka aure ni ko na kashe kaina - Bidiyon Budurwar da ta dinga suma tana rokar saurayinta ya aureta

- Wata budurwa ta kunyata kanta da saurayinta a kan wani babban titi na jihar Legas

- Budurwar ta suma yafi a kirga inda take rokar saurayinta akan ya taimaka ya aureta ko kuma ta kashe kanta

- Yayin da budurwar ke faman barka kuka akan saurayin, shi kuma saurayin yana ganin yaudarece da damfara budurwar ke son yi masa

Wata budurwa ta kunyata kanta da saurayinta a kan wani titi a jihar Legas, yayin da ta dinga birgima tana suma tana kuma rokar shi akan ya aureta ko kuma ta kashe kanta.

A wani da ya fara yawo a shafukan sada zumunta na zamani, ya nuna yadda budurwar take ta faman suma akan wata babbar hanya inda take yin magana cikin harshen turanci take cewa: 'Marry me or i die' ma'ana "Ka aure ni ko na kashe kaina."

KU KARANTA: To fah: Maza ne suke jawo yawan sake-saken da ke faruwa a kasar Hausa - Wani mutumi ya bayar da dalilanshi

Yayin da shi kuma wani matashi da aka hasko yana kuka shima yana cewa:

"Wannan yarinyar za ta sanya ni cikin matsala, wannan wane irin abu ne haka, wacc irin damfara ce kike yi haka," yayin da su kuma mutane suka taru a kansu suna kallon ikon Allah.

A yayin da mutane da yawan gaske suke ganin cewa soyayya a wannan lokaci batawa kai lokaci ce, ita kuma budurwar a lokacin take suma saboda tsananin soyayya da kaunar da take yiwa saurayin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel