To fah: Maza ne suke jawo yawan sake-saken da ke faruwa a kasar Hausa - Wani mutumi ya bayar da dalilanshi

To fah: Maza ne suke jawo yawan sake-saken da ke faruwa a kasar Hausa - Wani mutumi ya bayar da dalilanshi

- Wani mutumi mai suna Solomon Buchi ya bayyana cewa maza ne ummul aba'isin sake saken dake faruwa ga ma'aurata

- Ya ce da ace maza ne ke shan wahalar da mata ke sha a gidan aure da an samu raguwar kashe-kashen aure

- Ya ce mata ne ke yin duk wata wahala a cikin gida su maza aikinsu kawai suje su nemo kudi

A wani rubutu da wani mutumi mai suna Solomon Buchi ya wallafa a shafinsa na Twitter ya bayyana cewa maza ne suke kawo babbar matsalar da take sawa ake samun rabe-raben aure a kasar nan.

Mutumin ya ce: "Idan za a sanya maza su dinga irin wahalar da mata suke yi domin ganin sun zauna a gidan mazajensu da an samu raguwar sake-saken auren da kuma mata da yawa sun kasance cikin farin ciki. Ba zai yiwu mace ta daga wajen ganin aurenta ya inganta ba, sannan shi kuma mijin yana can yana batawa."

KU KARANTA: Kisan 'yan sanda: An gano wata takarda dake nuni da yadda rikici ke neman barkewa tsakanin 'yan sanda da sojoji

"Mace ce zata dafa abinci, ta yi shara, wanke-wanke, ita ce mai yin biyayya, ita ce mai yin addu'a, azumi kuma aikin namiji shine kawai ya fita ya nemo kudi, ya dinga bata doka, ya ci amanarta da kuma cin mutuncinta.

"Aure ana yin shi idan an samu fuskantar juna, aure ana yin shi tsakanin mutane biyu da zasu dage wajen ganin cewa sun zauna lafiya a gidan aurensu. Saboda haka duk namijin da ba zai iya ba ya hakura."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel