Gwamnatin Buhari ta sauya sunan hukumar kula da gidajen yarin Najeriya

Gwamnatin Buhari ta sauya sunan hukumar kula da gidajen yarin Najeriya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya canza sunan hukumar kula da gidajen yarin Najeriya zuwa hukumar gayaran halayya na Najeriya, inji rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Buhari ya sauya wannan suna ne bayan rattafa hannu kan wata sabuwar doka da ta raba hukumar zuwa bangare biyu, akwai bangaren dake kula da garkame masu laifi, da kuma bangaren da zai gudanar da ayyukan da basu shafi kama masu laifi ba.

KU KARANTA: Asirin Sojan daya kashe Yansanda 3 a Taraba kuma ya tseratar da Wadume ya tonu

Babban hadimin shugaban kasa a kan majalisar dattawa, Sanata Ita Enang ya bayyana cewa bangaren daya shafi garkame masu laifi yana da ayyuka kamar haka:

a – Ajiye mai laifi a cikin halin tsaro da aminci

b – Jigilar wanda suke rike dashi daga kotu zuwa da komawa

c – Duba yiwuwar inganta tsare tsaren gyara halayan wadanda suke rike dasu

d – Aiwatar da tsare tsaren gyara halayyan wadanda suke rike dasu tare da shiryasu don komawa cikin jama’a

e – Horas da wadanda suke rike dasu sana’o’in hannu da nufin su tsaya da kafarsu idan sun kammala wa’adinsu

f – Kula da gidajen horon kananan yara

g – Samar da hanyoyin kammala shari’a wadanda ake tuhuma ba tare da bata lokaci ba

Haka zalika wannan sabuwar doka ta baiwa shugaban hukumar na jaha damar kin karbar masu laifi a gidajen gyaran halayya idan har sun cika, don magance matsalar cunkoson gidajen.

Duk da haka dokar ta baiwa Alkalin Alkalai daman mayar da hukuncin kisan daya dauki tsawon shekara 10 ba’a aiwatar dashi ba zuwa hukuncin daurin rai da rai.

Daga karshe shugaba Buhari ya rattafa hannu kan dokar sauya sunan jami’ar gwamnatin tarayya ta noma dake garin Makurdin jahar Benuwe zuwa Jami’ar Joseph Sarwuan Tarka, Makurdi don tunawa da tsohon dan siyasan Arewa ta tsakiya, Joseph Tarka.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel