Yansanda sun cigaba da farautar Wadume wurjanjan, sun kwace gidajensa da motoci

Yansanda sun cigaba da farautar Wadume wurjanjan, sun kwace gidajensa da motoci

Jami’an tsaro bisa umarnin kwamitocin da aka kafa don binciken bahallatsar data biyo bayan harin da Sojoji suka kai ma Yansanda a garin Ibbi na jahar Taraba wanda ya yi sanadiyyar mutuwar Yansanda 3, da tserewar wani barawon mutane, Wadume, sun cigaba da farautar Wadume wurjanjan.

Yansanda uku da suka mutu sun hada da Inspekta Mark Ediale, Sajan Usman Danazumi, da Dahiru Musa, wanda a yanzu haka an garzaya da gawarwakinsu zuwa babban birnin tarayya Abuja don binciken gawarwakin, sai kuma wasu Yansanda 2 da suka jikkata wanda suma an mayar dasu Abuja don samun kulawa.

KU KARANTA: Zan zamo garkuwa ga talakan Najeriya a sabon wa’adin mulkina – Buhari

Jaridar The Nation ta ruwaito zuwa yanzu jami’an tsaro sun fara kwace wasu kadarorin da Hamisu Bala Wadume ya mallaka da suka hada da gidaje da motoci, daga ciki har da gidajen daya gina ma yan uwa da abokan arziki, da kuma motoci guda 20, daga ciki har guda 13 mallakin kamfanin sufurinsa.

Haka zalika abokansa, yan uwansa, da ma’aikatansa duk sun tsere daga jahar Taraba don gudun kada a kamasu a sakamakon binciken da ake gudanarwa a kan mutumin da yayi sanadiyyar tsatstsamar dangantaka tsakanin Yansanda da Sojoji.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Wadume mutum ne mai dogon buri, wanda baya ga kasancewa ya mallaki tarin motocin sufuri, yana da kuma burin shiga siyasa, hakan tasa ya fara gwadawa a zaben 2019 inda ya nemi takarar kujerar majalisar dokokin jahar Taraba mai wakiltar Ibbi a jam’iyyar YDP, amma bai ci ba.

Bugu da kari da ba dan farautarsa da ake yi ba, da masarautar Ibbi ta nadashi sarautar sarkin matasa a yayin bikin babbar Sallah, bincike ya nuna ya sakan ma fadar masarautar kudi don samun wannan sarauta.

Daga karshe kwamitocin binciken sun kama jami’in Sojan daya jagoranci kai ma Yansandan hari, tare da wasu Yansanda guda biyu dake ofishin Yansandan garin Ibbi, dukansu suna Abuja.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel