Wani sabon bala'in: Matasan Najeriya na shan fitsari don su bugu - NDLEA

Wani sabon bala'in: Matasan Najeriya na shan fitsari don su bugu - NDLEA

- Hukumar yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi ta kasar nan ta bayyana wata hanya da matasa ke bi a kasar nan wajen buguwa

- Bayan sanya doka akan shigo da kwayoyi irinsu Codeine wanda yasa da yawa daga cikinsu suka kara tsada a kasuwa

- Yanzu matasan sun samo wasu sababbin hanyoyi da suke bi wajen hada abubuwan da za su dinga buguwa cikin kudi kalilan

Hukumar yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi (NDLEA) ta bayyana wata sabuwar hanya da matasa a kasar nan suke bi domin buguwa.

Shugaban hukumar NDLEA na jihar Adamawa, Sheh Dankolo, ya bayyana cewa wasu matasan Najeriya suna shan fitsari wanda yake sawa su bugu, hakan ya biyo bayan hana shigo da kwayoyi da aka yi wanda yasa da yawa daga cikinsu su ka kara kudi a kasuwa.

KU KARANTA: Bidiyo: Sadiya Haruna ta tona asirin Alasan Kwalle da yadda yaso yin zina da ita a masana'antar Kannywood

"Akwai wasu daga cikin kwayoyi irinsu Codeine da gwamnatin tarayya ta tsaurara doka a kansu. Da yawa daga cikin kamfanoninsu sun rufe. Hakane yasa maganin mura da a da yake naira 250 kwalba daya yanzu ya zama naira 4,000. Haka zalika tramadol wacce take naira 50 yanzu ta koma naira 500.

"Saboda hana shigo da wannan kaya yasa suka zama babu su kuma suka kara kudi, yanzu haka mutane sun shigo da wata sabuwar hanya.

"Suna bin wata sabuwar hanya wajen sarrafa fitsari su dinga sha, sannan suna sanya maggi a cikin abubuwan sha suna buguwa. Haka zalika akwai wata alawa da suke sakawa a ruwa su bari tayi wasu kwanaki sai su dauka su dinga sha. Wannan dalilin ne yasa kawo karshen shaye-shaye zai yi wahala a kasar nan."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel