Wasu hazikan sojojin Najeriya sun kwanta dama yayinda Boko Haram suka kai hari bariki

Wasu hazikan sojojin Najeriya sun kwanta dama yayinda Boko Haram suka kai hari bariki

Dakarun sojojin Najeriya hudu da suka bi sahun takwarorinsu domin yakar wani hari da yan ta’addan Boko Haram suka kai bariki, sun kwanta dama a jihar Borno, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da ake shirye-shiryen bukukuwan babban Sallah, wato a ranar Asabar, inda yan ta’addan na Boko Haram suka afkawa barikin sojoji dake Gubio, jihar Borno.

Majiyar mu ta shaida mana cewa duk da sojojin sun yi kokarin fatattakar yan ta’addan amma abin bai yiwu ba haka suka arce bayan sun kashe sojojin.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa wani kwamandan sojojin ya bayyana cewa zuwa yanzu babu barikin sojoji ko daya a garuruwan Gubio, Magumeri da Kareto wanda hakan barazana ce babba ga mazauna wannan yankin.

Harin da aka kaishi da misalin karfe shida na yamman Asabar, yayi sanadiyyar mutuwar sojoji sannan yan ta’addan sun arce da manya-manyan motocin yaki da bindigogi da dama.

KU KARANTA KUMA: Kisan yan sanda: Kwamitin bincike ya kama sojoji 5 da jami’an yan sanda 2 a Taraba

Akwai rahoton da ya nuna cewa an gano daya daga cikin manyan motocin yakin da suka arce da a cikin daji sun jefar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel