Kisar 'Yan sanda 3: Jami'an tsaro sunyi dirar mikiya a Ibbi, sun kama mutane da dama

Kisar 'Yan sanda 3: Jami'an tsaro sunyi dirar mikiya a Ibbi, sun kama mutane da dama

Jami'an Rundunar 'Yan sandan Najeriya sun dira garin Ibbi bayan kashe jami'ansu uku da wani farin hula daya da sojoji su ka yi a titin da ya rantsa garin zuwa Wukari.

Daily Trust ta ruwaito cewa jami'an 'yan sandan da suka tafi garin sun kama mutane da yawa.

'Yan sandan sun tafi garin ne domin farautar wani da ake zargi da laifin garkuwa da mutane mai suna Alhaji Hamisu Wadumi da ya tsere a dai-dai wurin da aka kashe 'yan sandan uku da faran hula daya.

DUBA WANNAN: Abun kunya: Dan majalisar PDP ya yi wa wata mata zigidir a bainar jama'a

Wata majiya ta shaidawa Daily Trust cewa mataimakin kwamishinan 'Yan sanda Abba Kyari ne ya jagoranci tawagar 'yan sandan.

An gano cewa wasu daga cikin wadanda aka kama suna ofishin 'yan sanda da ke Wukari yayin da wasu kuma aka tafi da su zuwa Jalingo.

Motoccin sojoji da na 'yan sanda fiye da 15 ne suka isa Ibbi kuma suna cigaba da kama mutane a lokacin rubuta wannan rahoton.

An kuma gano cewa jami'an 'yan sandan sun kwato motocci da yawa da aka ce mallakar wanda ake zargi da garkuwa da mutanen ne a gidansa da kuma wasu wurare a garin.

Mazauna garin na Ibbi da ke kusa da Rafin Benue sunyi hijira daga gidajensu domin tsoron abinda zai kai ya kawo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel