Tashin hankali: Saurayi da budurwa sun mutu bayan sun fado daga kan gada lokacin da suke rungume-rungume da sunbatar juna

Tashin hankali: Saurayi da budurwa sun mutu bayan sun fado daga kan gada lokacin da suke rungume-rungume da sunbatar juna

- Wani bidiyo ya bayyana yadda wani saurayi da budurwa suka fado daga kan wata doguwar gada yayin da suke sumbatar juna da rungume-rungume

- Rahotanni sun bayyana cewa saurayi da budurwar sun dawo daga yawon holewa ne da suka je wani kulob a kasar Peru da daddare misalin karfe 1

- An bayyana cewa matar ta mutu a take a wajen, inda shi kuma namijin ya mutu bayan an garzaya dashi asibiti

Wata kyamara da aka sanya ta bayyana yadda wani lamari marar kyan gani ya faru, inda ta nuna yadda wani saurayi da budurwa suka gamu da ajalin su bayan sun fado daga kan wata doguwar gada lokacin da suke rungume-rungume da sumbatar juna a kasar Peru.

Mutanen wadanda aka bayyana sunansu da Maybeth Espinoz da kuma Hector Vidal an bayyana cewa suna kan hanyarsu ta komawa gidane daga yawon holewa da suka je wani kulob mai suna Cusco ranar Asabar dinnan da ta gabata, inda suka fado daga kan gadar Bethlehem mai nisan kamu hamsin 50ft da misalin karfe 1 na dare.

KU KARANTA: Wani soja da aka kora a aiki saboda ya harbi shugabanshi, an sake cafke shi da laifin fashi da makami a jihar Kaduna

A cikin bidiyon, saurayi da budurwar, an nuno su sun jingina a jikin karfen gadar suna sumbatar junansu, inda ita kuma macen ta zame ta fada kuma ta ja saurayin shima ya bita.

A rahoton da jaridar Panamerica ta ruwaito, matar ta rasa ranta a take a wajen, inda shi kuma namijin ya samu raunika da karaya amma daga baya shima ya mutu a asibiti.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel