Tashin hankali: Ko kadan bana dana sanin kashe mahaifina dana yi, saboda shi ma da ya samu dama kashe ni zai yi - Aminu

Tashin hankali: Ko kadan bana dana sanin kashe mahaifina dana yi, saboda shi ma da ya samu dama kashe ni zai yi - Aminu

- Wani mutumi dan shekara 40 a duniya ya bayyana cewa ko kadan baya nadamar kashe mahaifinsa da yayi

- Ya ce ya kashe mahaifin nasa ne saboda ya gano cewa dan kungiyar asiri ne, kuma yana neman kowacce hanya da zai yi shima ya kashe shi

- Ya ce a shirye yake ya fuskanci duk wani hukunci da aka yanke masa

Wani mutumi dan shekara 40 a duniya, mai suna Bisso Aminu, ya bayyana cewa ko kadan baya dana sanin kashe mahafinsa da yayi mai suna Aminu Allahbani, dan shekara 65.

A cewar Aminu, mahaifin nasa matsafi ne, kuma da ace bai kashe shi ba da tuni shima yayi amfani da jininshi wajen tsaface-tsafacenshi.

Jami'an 'yan sanda ne dai suka samu nasarar kama Aminu, bayan yayi amfani da fartanya ya kashe dattijon mahaifin nasa har lahira a lokacin da yake yin bacci.

Da yake magana da manema labarai, Aminu ya bayyana cewa ko kadan bai nadamar kashe mahaifin nasa ba, kuma a shirye yake ya fuskanci dukan hukuncin da ya dace dashi.

KU KARANTA: Anyi ba ai ba: Wata 'yar madigo ta kashe kanta saboda abokiyar iskancinta ta mutu

"Bana nadamar kashe mahaifina ko kadan, saboda inda ace ban kasheshi ba da tuni ya kashe ni. Baya kaunata kwata-kwata saboda duk wata hanya da zai bi yaga yayi amfani dani wajen tsafinsu yayi ya kasa a kaina saboda na fishi wayo, kuma da ace bai nemi ya kashe ni ba babu yadda za ayi na kashe shi. A shirye nake na karbi duka hukuncin da ya dace dani." in ji shi.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar 'yan sandan, DSP Mohammad Abubakar, ya ce zasu mika mai laifin zuwaa kotu bayan sun kammala bincike akan shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel