Buhari ya halarci bikin yaye daliban kwalejin horas da manyan hafsoshin Sojoji (Hotuna)

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu halartar bikin yaye daliban manyan hafsoshin tsaron Najeriya dake babban birnin tarayya Abuja, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Wannan biki dai shine karo na 27 da kwalejin ta yaye dalibanta, manyan hafsohin tsaro daga hukumomin tsaro daban daban na Najeriya, musamman daga rundunar Sojan kasa, ruwa da ta sama.

KU KARANTA: Direban Dangote ya tseratar da daruruwan dalibai daga rikicin kabilanci a jahar Taraba

Buhari ya halarci bikin yaye daliban kwalejin horas da manyan hafsoshin Sojoji (Hotuna)
Buhari ya halarci bikin yaye daliban kwalejin horas da manyan hafsoshin Sojoji
Asali: Facebook

A yayin bikin Buhari ya baiwa dalibin da yafi hazaka daga cikin daliban da aka yaye, kyauta, wannan dalibi shine GC OC Obadike, sa’annan shina shugaban kasa Buhari ya samu kyauta daga babbar sakatariyar ma’aikatar tsaro ta Najeriya, Nuratu Batagarawa.

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, babban hafsan tsaro na Najeriya, Janar Abayomi Olanisakin, shugaban kwamitin tsaro na majalisar dattawa, Sanata Jimi Benson, babban hafsan rundunar Sojan kasa, Laftanar janar Tukur Yusuf Buratai.

Sauran sun hada da babban hafsan sojan sama, Sadique Abubakar, babban hafsan sojan ruwa, Ite Ibas, babban sufetan Yansandan Najeriya Abubakar Adamu da kuma shugaban hukumar tsaro ta DSS, Yusuf Magaji Bichi.

Ga yadda bikin ya kasance nan a cikin hotuna:

Buhari ya halarci bikin yaye daliban kwalejin horas da manyan hafsoshin Sojoji (Hotuna)
Buhari ya halarci bikin yaye daliban kwalejin horas da manyan hafsoshin Sojoji
Asali: Facebook

Buhari ya halarci bikin yaye daliban kwalejin horas da manyan hafsoshin Sojoji (Hotuna)
Buhari ya halarci bikin yaye daliban kwalejin horas da manyan hafsoshin Sojoji
Asali: Facebook

Buhari ya halarci bikin yaye daliban kwalejin horas da manyan hafsoshin Sojoji (Hotuna)
Buhari ya halarci bikin yaye daliban kwalejin horas da manyan hafsoshin Sojoji
Asali: Facebook

Buhari ya halarci bikin yaye daliban kwalejin horas da manyan hafsoshin Sojoji (Hotuna)
Buhari ya halarci bikin yaye daliban kwalejin horas da manyan hafsoshin Sojoji
Asali: Facebook

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel