Allah Sarki: Wani kare ya shekara daya da rabi yana gadin inda mai gidansa ya mutu

Allah Sarki: Wani kare ya shekara daya da rabi yana gadin inda mai gidansa ya mutu

- Wani kare ya shekara daya da rabi yana gadin wajen da ubangidansa yayi hadarin mota ya mutu

- Karen wanda daga baya mutane suka gano halin da yake ciki an koreshi daga wajen lokuta da dama amma da ya tafi sai ya dawo

- Daga baya mutanen yankin suka hakura suka dingakai masa abinci yana ci, daga ya gama kuma sai ya dawo wajen

Wani kare ya sanyawa mutane da yawa tausayi a zukatansu bayan an gano cewa yayi watanni 18 yana kwana a gefen hanyar da ubangidansa ya mutu sanadiyyar hadarin mota.

Karen wanda ake yiwa lakabi da suna Greek Hachiko yana matukar son ubangidan nasa. Karen wanda yake jinsin Akita ne yayi jiran shekara daya da rabi a wajen da mai gidan nasa ya mutu sanadiyyar hadarin mota da yayi a kusa da tashar jirgi dake kasar Japan.

Rahotanni sun nuna cewa, karen wanda yake da launin fari ya rayu sama da watanni 18 a gefen hanyar zuwa birnin Greek a Nafpaktos dake kasar Girka.

Wasu mutane sun yi iya bakin kokarinsu domin ganin sun kori karen daga wajen amma lamarin ya ci tura.

KU KARANTA: Ba sani ba sabo: An dakatar da shugaban karamar hukuma da Hakimi a jihar Zamfara

Haris wanda yake mamallakin karen ya rasu yana da shekaru 40 a duniya, inda mutuwar tashi ta razana mutane da dama.

Rahotanni dai basu bayyana ko karen yana cikin motar ba lokacin da hadarin ya faru, kuma ba a san yadda aka yi ya san inda hadarin motar ya faru ba. Sai dai mutane sun tabbatar da cewa karen yana zama ne a kusa da inda Haris din ya rasu.

Bayan jama'ar garin sun gano halin da karen yake ciki sai suka fara kawo masa abinci, amma da ya gama cin abinci sai ya sake dawowa wajen ya yi kamar yana jiran ubangidan nasa ya taso su tafi gida.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel