Tirkashi: Zan tona asirin yadda muka yi magudin zabe a Kano, uban kowa ma ya rasa - Abdulmumini Jibrin

Tirkashi: Zan tona asirin yadda muka yi magudin zabe a Kano, uban kowa ma ya rasa - Abdulmumini Jibrin

- Dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Kiru da Bebeji yayi barazanar tona asirin magudin zaben jihar Kano

- Ya ce matukar ba a daina takura mishi ba to zai fito ya bayyana kowa ma ya rasa

- Jiya ne dai jam'iyyar APC mai mulki ta dakatar da dan majalisar daga jam'iyyar na tsawon watanni goma sha biyu

Dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Kiru da Bebeji, Hon. Abdulmumini Jibril Kofa, yayi barazanar tona asirin hanyoyin da suka bi suka gabatar da magudin zabe a jihar Kano.

Jiya ne dai babbar jam'iyyar APC mai mulki ta dakatar da dan majalisar daga jam'iyyar na tsawon watanni goma sha biyu, bayan ta zarge shi da yi mata zagon kasa.

A lokacin da yake mayar da martani, Kofa ya bayyanawa manema labarai cewa a shirye yake ya tona asirin duk abinda ya faru a jihar dan kowa ma ya rasa.

KU KARANTA: Da duminsa: Shugaba Buhari da jam'iyyar APC sun bayyana samun nasarar shari'ar zabe tun kafin kotu ta yanke hukunci

"Zan fito na fadawa duniya ainahin abinda ya faru a jihar Kano, ma'ana zan bayyana yadda muka yi magudin zabe matukar aka cigaba da takura mini," in ji dan majalisar.

Tun bayan kammala zaben gwamna a jihar Kano dai aka fara samun takun saka tsakanin dan majalisar da shugabannin jam'iyyar APC ta jihar Kano, inda suka jima suna mayarwa da juna bakaken maganganu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel