Zan yi takarar shugaban kasa a 2027 – Sanata Dino Melaye

Zan yi takarar shugaban kasa a 2027 – Sanata Dino Melaye

Sanata Dino Melaye mai wakiltan yankin Kogi ta Yamma a majalisar dattawa, a ranar Laraba, 31 ga wata Yuli, ya ziyarci babban birnin jihar a yunkurinsa na son tsayawa takaran gwamnan jihar.

Sanatan ya fara ne da ganawa da manyan yan jam’iyyar PDP a Sakateriyar jam’iyyar da ke Lokoja, kuma har ila yau ya tafi cibiyar manema labarai inda ya gabatar da manufofinsa akan jihar.

Melaye yace muradinsa na shugabantan jihar ba wai ceto jihar daga gwamna mai ci bane kadai illa son gina sabon Kogi tare da shugabanci mai dauke da shawarwarin kwararru.

Sanata Melaye har ila yau yace idanunsa na akan kujerar shugabancin kasa a 2027, inda ya karfafa cewa takaransa na gwamna ta kasance tamkar matattakala ga ra’ayinsa na son shugabancin kasa.

Ya kuma bayyana cewa daga cikin yan takara a jam’iyyar PDP, ya kasance mafi kyau kuma mafi kwararre wajen ceto jihar daga hannun wanda ke rike da ita a yanzu.

KU KARANTA KUMA: Tirkashi: Shugabannin Arewa bakaken munafukai ne - Shehu Sani

Dan majalisar dokokin kasar ya kuma bukaci kungiyar NUJ da ta shirya muhawaran yan takaran gwamna a jam’iyyar don baiwa jihar damar zaban dan takaransu, inda yake cewa takaran Gwamna yana da muhimmanci kwarai da gaske, saboda haka baza a bar shi a hannun yan siyasa ba kadai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel