Kotun koli za ta zauna a 20 ga Watan Agusta domin shari’ar Buhari da Atiku

Kotun koli za ta zauna a 20 ga Watan Agusta domin shari’ar Buhari da Atiku

An dage sauraron karar da ‘dan takarar shugaban kasar Najeriya na zaben 2019 a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya kai gaban kotun koli inda ya ke kalubalantar shari’a da a ke yi a kotun zabe.

A Ranar 30 ga Watan Yuli, 2019, babban kotun Najeriya ta dage zaman da ta ke yi domin sauraron korafin da Atiku Abubakar ya kawo na neman a yi watsi da hukuncin da Alkali Garba Muhammad ya yi.

Babban Lauyan ‘dan takarar na PDP, Paul Erokoro, ya nemi kotu ta karbi wasu karin hujjoji da bayani daga gare sa. Wannan ya jawo shari’ar ta tsaya cak inda sauran Lauyoyi su ka nemi a kara masu lokaci.

A wani mataki da kotun ta fara dauka, za a dakatar da zaman wannan shari’a sai zuwa Ranar 20 ga Watan gobe na Agusta. Alkali mai shari’a Mary Peter-Odili da wasu Alkalai su dauki wannan hukunci.

KU KARANTA: Kotun zabe ta ba wasu Gwamnonin PDP gaskiya a zaben 2019

A Ranar jiya Talata ne mai shari’a Mary Peter-Odili ta nemi a dakatar da sauraron wannan kara zuwa nan da mako uku. Kafin wannan lokaci wadanda a ke tuhuma za su kammala duk binciken da su ke yi.

Babban Alkalin da ke sauraron korafin zaben shugaban kasa na 2019, Mai shari’a Garba Mohammed ya yi watsi da wani roko da Lauyoyin PDP su ke yi na bada dama su duba uwar-garken INEC.

Jam’iyyar PDP ta hakikance a kan cewa ita ce ta lashe zaben shugaban kasa kamar yadda kuri’un da hukumar zabe na INEC ta tattara a uwar-garken ta su ka nuna. INEC ta karyata wannan ikirari a gaban kotu.

Yunus Usman shi ne Lauyan da ke kare hukumar zabe a kotu, yayin da shi kuma babban Lauya Wole Olanipekun, ya ke kare shugaban kasa. Lateef Fagbemi, shi ne Lauyan APC a wannan kara.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel