Tashin hankali: Na yi zina da 'yan mata kanana sama da 2500 a rayuwata - Jarumi Oboy Siki

Tashin hankali: Na yi zina da 'yan mata kanana sama da 2500 a rayuwata - Jarumi Oboy Siki

- Wani fitaccen jarumin fim na kasar Ghana Oboy Siki ya bayyana wani boyayyen sirri na rayuwarsa

- Ya bayyana cewa ya kwanta da sama da 'yan mata dubu biyu da dari biyar (2500), kuma duka 'yan shekara 16 ne

- Ya ce zina ta riga ta zame masa jiki, domin kuwa mahaifinsa ma haka yake, saboda haka yana matukar son mata

Jarumi Oboy Siki ya bayyana wani boyayyen lamari game da rayuwarsa, inda ya bayyana cewa yayi zina da sama da mata dubu biyu da dari biyar a rayuwarsa.

A cewar fitaccen jarumin, ya ce yana matukar son yara mata kanana, kuma idan har yace bai son kananan 'yan mata ya yiwa kanshi karya ne.

Oboy Siki wanda yayi hira da manema labarai bayyana cewa neman mata yana jikinshi ne, domin kuwa mahaifinsa ma mazinaci ne, saboda haka yana matukar son mata.

KU KARANTA: Allah Sarki: Wata mata ta ba wa tsohon mijinta Qodarta guda daya bayan shekara biyar da rabuwarsu

Ya cigaba da cewa, da yana da littafi da yake daukar sunayen matan da ya kwanta da su, amma yana kai wa 2500, sai ya yanke shawarar dai na neman mata.

Oboy Siki bai tsaya a nan ba, ya cigaba da a Ghana yana iya kwanciya da mace a kowanne lungu da sako na fadin kasar, kuma shi baya kwanciya da tsofaffin mata, yana kwanciya da yara 'yan shekara 16 ne.

A cewarsa, 'yan shekaru 16 sun riga sun gama balaga, kuma yana bai wa 'yan majalisar kasar shawara suyi sauri su rage shekarun balaga daga shekara 18 zuwa 16.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel