Kudi masu gidan rana: An sayar da hoton da yafi kowanne tsada a duniya akan sama da naira biliyan biyu (N2b)

Kudi masu gidan rana: An sayar da hoton da yafi kowanne tsada a duniya akan sama da naira biliyan biyu (N2b)

- An sayar da wani hoto akan kudi dalar Amurka miliyan shida da rabi, inda ya kai kimanin naira biliyan biyu da wani abu

- Hoton dai an dauke shi a shekarar 2014 a cikin wani kogon dutse na kasar Amurka

- Hoton yana nuni da yadda qura take wucewa ta cikin haske wanda Peter Lik ya dauka mai ban sha'awa

Wannan hoto da yake nuna yadda qura take shigewa ta cikin haske an dauke shi a wani kogo dake Grand Canyon na kasar Amurka sannan an sayar dashi akan farashi mai tsadar gaske.

Kudi masu gidan rana: An sayar da hoton da yafi kowanne tsada a duniya akan sama da naira biliyan biyu (N2b)
Peter Lik
Asali: Facebook

Hoton wanda Peter Lik ya dauka a shekarar 2014 ya bar tarihi sosai, yayin da aka sayar da shi akan kudi dala miliyan shida da dubu dari biyar ($6.5m), inda kudin ya kai sama da naira biliyan biyu (N2b) a kudin Najeriya.

KU KARANTA: Tamu ta samu: An ba wa 'yar Najeriya mukamin mininsta a kasar Birtaniya

Harkar daukar hotuna abu ne mai ban sha'awa da yake da hanyoyi masu dumbin yawa. Harkar daukar hoto yana kara jawo hankalin mutane a wannan lokutan suji suna son shiga harkar.

Idan ba a manta ba a kwanakin baya mun kawo muku labarin yadda aka sayar da wata wasika ta fitaccen mawakin nan Tupac Shakur, wacce ya rubutawa budurwarshi Madonna a lokacin da yake gidan yari da nufin yana so su rabu.

Bayan rubuta wasikar tashi ba jimawa ne Tupac ya mutu, inda kuma aka sayar da wasikar tashi akan kudi sama da naira miliyan dari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel